Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, ya ce yanzu abu ne mai wahala samun mutane masu nagarta.
Farfesa Osinbajo ya bayyana hakan a wajen bikin ɗaukar sabbin ɗaliban shekarar 2024 na Jami’ar Miɓa Open a Abuja, a ranar Asabar.
Yayin da yake kare Jami’ar, wanda ya bayyana a matsayin makomar kawo ingantacciyar ilimin gaba da sakandare a Afirka, ya ce ba za a iya isar da ingantaccen ilimi a Afirka ba ga yawancin masu sha’awar samun digirin jami’a idan za a ci gaba da gina jami’o’in gargajiya domin ɗaukar su.
Ya ce: “Kowace shekara, fiye da mutum miliyan 1.7 suna rubuta jarrabawar UTME da Hukumar JAMB ke gudanarwa, kuma matsakaicin mutum 400,000 ne kawai ke samun guraben shiga jami’o’i. Don haka akwai miliyan 1.3, mafi yawanci matasa, da suke cancanta amma ba su da dama na samun ilimin jami’a.”
Yayin da yake taya ɗaliban murna, Osinbajo ya buƙaci su tafi su samu cikakken nasara, yana cewa, “Wannan cikakken nasara ba kawai yin nasara na ‘yan shekaru ba ne ko tara mabiya a intanet na wani lokaci. Cikakken nasara ita ce barin tasiri mai ɗorewa ta hanyar aikinka, gudunmawarka ga al’umma, ko ƙimar da za ka iya koyarwa ga wasu.”
Osinbajo ya koka kan yadda ake samun ƙarancin mutane masu gaskiya da kima inda ya bayyana cewa ko satar kuɗi mutum ya yi, yana wahalar samun mutumin da zai ajiye masa kuɗin bisa gaskiya.
