APC za ta karɓe dukkan jihohin Kudu maso Yamma – Ganduje

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki za ta karɓe iko a yankin Kudu maso Yamma ta hanyar lashe zaɓen gwamna da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba a Jihar Ondo.

Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya jagoranci shugabancin  jam’iyyar APC na ƙasa zuwa taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Akure, babban birnin jihar, a ranar Lahadi.

Jaridar Manhaja ta rawaito cewa, Shugaban APC na kasa ya samu rakiyar gwamnoni da suka haɗa da Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Abiodun Oyebanji (Ekiti), da Dapo Abiodun na Ogun, wanda Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Talabi Olatokunbo ya wakilta.

Yayin da ya ke magana a taron, Ganduje ya ce jam’iyyar mai mulki tana aiki tuƙuru don tabbatar da cewa ta bazu gabanin zaɓen gama-gari na 2027.

Ya jaddada cewa dole ne a kama jihohin Oyo da Osun domin ƙarfafa goyon bayan Shugaba Bola Tinubu, musamman a yankin Kudu.

Sai dai ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta bayyana dabararta ta lashe jihohin yankin ba, inda ya yi kira ga shugabannin APC su haɗa kai don tabbatar da haɗin kai tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Ya ce zaɓen gwamna a Ondo ba wata matsala ba ce ga APC, yana mai cewa dukkanin shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa sun bayar da cikakken goyon bayansu ga Gwamna mai ci, Lucky Aiyedatiwa.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Osun, Mista Sunday Bisi, ya gargaɗi Shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, da ya guji yin furucin da zai iya tayar da tarzomar siyasa a yankin Kudu maso Yamma.

Manhaja ta rawaito cewa Bisi, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, yana mayar da martani ga kalaman da Ganduje ya yi a wajen taro a Jihar Ondo, inda aka rawaito ya ce jam’iyyarsa na da dabarar “mamaye” dukkanin yankin Kudu maso Yamma.

Shugaban PDP ya gargaɗi Ganduje cewa irin waɗannan kalaman na iya tayar da hankulan jama’a da haifar da rashin zaman lafiya a ƙasar.

Ya kuma jaddada cewa mutanen Osun za su yanke hukunci kan wanda zai mulke su idan lokacin ya yi.

Yayin da yake bayyana kalaman Ganduje a matsayin “ƙoƙari na jefa yankin Kudu maso Yamma cikin rikicin siyasa da ba ya da amfani,” Bisi ya gargaɗi cewa Nijeriya, da tuni take fama da rikice-rikicen ƙabilanci da ƙalubalen tattalin arziki, bai kamata a ƙara tayar mata da hankali ba.

Bisi ya ce, “Ga mutum wanda bai iya cin zaɓe a jiharsa ta Kano ba, saboda rashin iya mulki a wa’adinsa a matsayin gwamna, ya zo yanzu yana barazanar zuga yankin Kudu maso Yamma da wuta da hayaki ba kawai rashin hankali ba ne, amma rashin tunani ne kwata-kwata.

“Yayin da Shugaban ƙasa ke ci gaba da fuskantar matsalar tattalin arzikin ƙasar, Ganduje ya kamata ya yi taka-tsan-tsan kada ya ƙara dagula lamarin ta hanyar ƙoƙarin yin maguɗi a zaɓen, musamman a yankin Kudu maso Yamma. Yin hakan zai zama tamkar taka kan maciji mai haɗari.

“Idan Ganduje ya kasa, kamar yadda ya yi, wajen tayar da rikici a Kano, inda aka yi watsi da APC saboda mulkinsa mai tsanani, ya kamata ya shirya karɓar irin wannan sakamakon a wasu jihohin da APC ta kasa gamsar da masu zaɓe.”

By ukarofi