An sace mutanen ƙauyensu guda 17 da haɗin bakinsa
Daga UMAR GARBA a Katsina
Jami’an tsaron gwamnatin Jihar Katsina na KSCWC sun samu nasarar cafke wani mai suna Alhaji Salisu Abdul’aziz Runka, wanda ƙwararren mai bai wa ɓarayin daji bayanan sirri ne.
A cikin wani bidiyo da Blueprint Manhaja ta bibiya, wanda wani ɗan jarida a Katsina da ke bincike kan aikata miyagun laifuka ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, an ga Alhaji Runka yana iƙirarin cewa shine ke bai wa ‘yan bindinga bayanan ƙauyen Runka dake ƙaramar Hukumar Safana ta jihar Katsina.
“Ni Alhaji Salisu Abdul’aziz Runka na yi alƙawarin zan faɗa wa hukuma laifin da nake aikatawa tun daga farko har zuwa ƙarshe.
“Yau asirina ya tonu saboda haka na yi alƙawarin yin bayani game da yadda nike aikin infoma,” inji Runka.
Wanda ake zargin ya amince cewa shine ke gayyato ɓarayin daji dake addabar yankin Runka.
Ya cigaba da cewa shine ke sanar da ɓarayin daji gidajen mutanen da ya kamata ‘yan bindingar su je don yin garkuwa ko kuma neman kuɗin fansa.
“Tunda na fara wannan aikin na gayyato ɓarayi inda suka sace mutane aƙalla 17 tare da kashe wasu mutum biyu.
“Yanzu dai an kama ni a matsayin infoma kuma na yarda da zargin da ake mini,” inji shi.
Da aka tambayi Runka ko dai tilasta ma shi aka yi don ya faɗi waɗannan bayanan sai ya ce.
“Ba wanda ya tursasa mani ni dai asiri na ya tonu kuma na yadda zan faɗa wa hukuma laifi na,” inji shi.
Daga nan sai wanda ake zargin ya bayyana manyan ‘yan bindingar da yake yi wa aiki.
“Cikin waɗanda na ke aiki da su aiki Alhaji Kachalla Ruga da Sani Moɗinge da Usman Mani Gurgu na ɗauki tsawon shekara huɗu ina aikin infomanci.
“Akwai mutanen da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su, waɗanda ni na taimaka a matsayin mai ba da bayanai domin sauƙaƙa sace su.
Ya ƙara da cewa kafin ‘yan bindingar su kawo farmaki a Runka, sai sun sanar da shi domin ya duba masu shige da ficen jami’an tsaro.
“A farmakin farko da ‘yan bindigar suka kai, Alhaji Ruga Kachala ya kira ni ya sanar da ni cewa za su shigo ƙauyen Runka domin su ɗauki mutane, na ba su bayanan mutane 12 da za su yi garkuwa da su a gidan Alhaji Ma’azu Runka.
“Na kuma ba su bayanan yadda za a ɗauke wasu mutum biyar a gidan Salmanu,” inji shi.
Alhaji Runka ya ce bayan kammala aikin da ya yi wa ‘yan bindingar sun ba shi Naira 400,000 a matsayin kason sa, daga cikin Naira miliyan 25 da karɓa a matsayin kuɗin fansa tare da babura biyu.
Daga ƙarshe Alhaji Salisu Runka, ya ce ya yi matuƙar nadama akan wannan mummunan laifi da yake aikatawa daga nan sai ya yi alƙawarin daina wannan aiki, amma fa idan ya samu kuɓuta daga komar jami’an tsaro da ya faɗa.
