Gwamnatin Gombe za ta gina makarantun sakandare 23, tare da ɗaukar ‘yan mata 8,000 duk shekara

Spread the love

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Gwamnatin Jihar Gombe, a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ta ƙaddamar da wani shiri na magance matsalar yawan ‘yan mata da ba sa zuwa makaranta, inda ta ƙuduri aniyar gina sababbin makarantun sakandare guda 23 da kuma ɗaukar ‘yan mata 8,000 duk shekara ta hanyar AGILE.

Da take magana da manema labarai, Dakta Amina Haruna Abdul, Koodinatan shirin AGILE na jiha, ta yaba wa gwamnan bisa goyon baya da kuma jajircewa kan ci gaban ilimin ‘ya’yan mata a Gombe.

Ta bayyana cewa shirin AGILE na da manufar ƙarfafa ‘yan mata ta hanyar samar musu da damar samun ilimi da koyon sana’o’i, don su zama masu ba da gudunmawa ga cigaban al’umma. Ta ce, “Ilmantar da yarinya na kafa tubalin gina al’umma mai inganci.”

Don magance wasu ƙalubale kamar talauci, shirin zai ba da tallafin karatu ga ‘yan mata 10,000 a shekara ta farko, wanda zai ƙara yawan masu cin gajiyar tallafin duk shekara har tsawon shekaru biyar. Kowace yarinya da aka zaɓa za ta riƙa samun tallafi a kowane zangon karatu don samun kayayyakin makaranta masu muhimmanci.

Dakta Amina ta bayyana cewa AGILE na shirin gina makarantun sakandare 26—13 na matakin farko da kuma 13 na mataki na biyu a yankunan da ke da buƙata, tare da kafa cibiyoyin koyon sana’o’i biyu a kowanne daga cikin ƙananan hukumomi 11 na jihar. Waɗannan cibiyoyi za su ba da horo na sana’o’i don tallafawa yaran da ba sa zuwa makaranta.

Haka kuma, shirin zai samar da kayan koyon zamani a cikin waɗannan sabbin makarantu da za a gina, ciki har da ɗakunan koyon kwamfuta, damar koyon shiga yanar gizo.

Bugu da ƙari, AGILE zai ƙunshi ɓangaren sauya ɗabi’u wanda zai taimaka wajen canza ra’ayin al’umma kan ilmantar da ‘yan mata.

Dakta Amina ta yi kira ga jama’a da su ba da goyon baya ga shirin AGILE, tana tabbatar da cewa tawagar shirin za ta kasance a shirye don amsa duk wani damuwa daga al’umma, don tabbatar da nasarar aiwatar da shirin.

By ukarofi