Gaggan ‘yan ta’adda ne suka hana gyaran wutar lantarki da ta lalace a Arewa – Barau

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce ‘yan ta’adda masu ɗauke da makamai sun mamaye wurare masu muhimmanci a kusa da tushen wayoyin wutar da suka lalace, waɗanda suka haifar da yanke wuta a jihohi da dama na Arewacin Nijeriya sama da mako guda.

Hakan ne ya hana a gudanar da gyare-gyare cikin gaggawa, in ji Barau Jibrin.

Manhaja ta rawaito cewa Barau Jibrin, wanda ya ce yana tattaunawa na tare da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, da Kamfanin Rarraba Wuta na Nijeriya (TCN) kan batun a jawabin da ya yi wa abokan aikinsa a majalisar dattawa a ranar Talata.

Ya ce TCN tana aiki tare da NSA da hukumomin tsaro domin dawo da wutar lantarki ga jihohin da abin ya shafa.

A makon da ya gabata, Kamfanin Rarraba Wuta na Nijeriya (TCN) ya ce layin wutar Shiroro-Mando ya fuskanci ɓarna, wanda ya haifar da katsewar wuta a kimanin jihohi 17 daga cikin jihohi 19 na Arewacin Nijeriya.

By ukarofi