Jan-ƙafa wajen yanke hukunci ga masu laifi barazana ce ga cigaban tsaro – Uba Sani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya jaddada muhimmancin ɓangaren shari’a da irin rawar da take takawa wajen yaƙi da matsalar tsaro a jihar.

Gwamnan ya ce jinkirin da ake samu wajen yanke wa waɗanda ake zargi da laifukan ta’addanci na ƙara ƙarfafa wa ‘yan ta’adda guiwa.

Don haka, gwamnan ya nuna akwai buƙatar mai da hankali daga ɓangaren masu ruwa da tsaki a fannin shari’a domin magance matsalar jan ƙafar da ake samu na wajen yanke hukunci a matsayin wani mataki na ƙarfafa wa yunƙurin gwamnati na tabbatar da tsaro a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin rantsar da mai shari’a Murtala Jafaaru Zubairu a matsayin alƙalin Babbar Kotu a cambar lauyoyi ta Sir Kashim Ibrahim a ranar Talata.

Gwamnan ya sha alwashin inganta wurin ayyukan ma’aikatan shari’a don jadadda fatan nagari da al’umma ke da shi ga ɓangaren shari’a da tallafa wa ilimin ma’aikatan shari’ar da ba wa al’umma damar neman haƙƙinsu.

“Daya daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatina ta sa a gaba shi ne inganta ɓangaren shari’a domin tabbatar da sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata saboda ɓangaren shari’a na da muhimmancin gaske wajen samar da zaman lafiya da cigaban dimokraɗiyya,” in ji gwamna Uba Sani.

Daga nan gwamnan ya shawarci sabon alƙalin kan mai da hankali wajen tabbatar da adalci ba tare da jin tsaro ba saboda rantsuwar da ya sha ta zai tabbatar da gaskiya ne da yanke hukunci ba tare da jan ƙafa ba.

Gwamna Uba Sani ya ce ana cutar da waɗanda aka kama da waɗanda suke da haƙƙi kan waɗanda aka kama idan aka jinkirta yi musu shari’a.

Ya kuma ya ba wa alƙalan jihar saboda yadda da aka yi da su a matsayin mafiya ƙwarewa a ƙasar nan tare da roƙonsu da su cigaba da yin riƙo da gaskiya kasancewar su ne waje na ƙarshe da al’umma suke da ƙarfin guiwa a kansu.

By ukarofi