An sako likitar da aka yi garkuwa da ita a Kaduna, Dakta Ganiyat, bayan wata 10

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Likitar nan da aka yi garkuwa da ita a Jihar Kaduna, Dakta Ganiyat Popoola ta shaƙi iskar ’yanci bayan shafe kimanin wata 10 a hannun ’yan bindiga.

Poppola, wadda take aiki a asibitin ido na ƙasa da ke Kaduna, an sace ne a ranar 27 ga Disamban shekarar 2023 tare da mijinta, Nurudeen Popoola wanda sojan sama ne da ɗan uwanta Folaranmi Abdul-Mugniy, amma a watan Maris aka sako mijinta, amma masu garkuwar suka ci gaba da riƙe likitar da ɗan uwan nata.

A watannin baya ne ƙungiyar Likitoci Masu Neman ƙwarewa suka shiga yajin aiki saboda nuna rashin daɗin su kan gaza ƙwato likitar a hannun masu garkuwa.

A ranar Laraba ne dai aka sako likitar da ɗan uwanta, kamar yadda shugaban ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta ƙasa, Dr Tope Zenith Osundara, ya bayyana, inda ya ce ba a biya kuɗin fansa ba.

By ukarofi