Ghana ta fara shirin sayen mai daga matatar Ɗangote

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Man Fetur na ƙasar Ghana ya ce, ƙasar za ta fara sayen man fetur daga matatar man Dangote ta Nijeriya da zarar matatar ta fara aiki gadan-gadan, don ta rage tsadar shigo da mai daga Turai.

Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Ghana, Mustapha Abdul-Hamid, ya ce hakan na iya kawo ƙarshen shigo da mai daga Turai na dala miliyan 400 duk wata.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, ya yi magana ne a wurin taron mai na OTL Africa Downstream a Legas.

Matatar Dangote da ke Lekki ta dala biliyan 20 ta fara sakin mai cikin kasuwar Nijeriya a ranar 15 ga Satumba, 2024.

Sai dai a wajen taron da aka gudanar a Legas a ranar Litinin, jami’in hukumar mai na Ghana ya bayyana cewa ƙasarsa na iya fara shigo da mai daga matatar mai ta Nijeriya.

By ukarofi