Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
An sake ɗauke wuta gaba ɗaya a babbar tashar lantarki ta Nijeriya. Babbar tashar wutar lantarkin ƙasar ta ɗauke wuta gabaɗaya ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Alhamis, lamarin da ya haddasa katsewar wuta a duk layukan rarraba wutar a faɗin Nijeriya.
Kimanin kwana biyu kenan bayan irin haka ta faru a ƙasar, duk a cikin watan nan na Nuwamba.
Wannan shine karo na 10 da wutar lantarki ta ɗauke a faɗin Nijeriya sakamakon lalacewar babbar layin lantarkin ƙasar a cikin wannan shekara ta 2024.
Zuwa lokacin da mu ka kammala wannan labari dai Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) ba ta bayyana musabbabin matsalar ba.
Amma Kamfanin Raba Lantarki na Jos, ya tabbatar cewa wutar da ya ke samu daga babban layin lantarki na ƙasa ya ɗauke gabaɗaya.
Kamfanin ya ce, “mu na sa ran komai zai dawo yadda ya ke da zarar an shawo kan matsalar.”
Binciken da aka yi a tashar ‘Nigerian System Operator’s Portal’ (niggrid.org) ya nuna cewa, samar da wutar lantarki ya ragu zuwa rashin megawat bakiɗaya da ƙarfe 11:30 na safe, wanda ya shafi kamfanonin samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar.
Wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki sun tabbatar da hakan a dandalinsu na sada zumunta.
“Don Allah mu na sanar da ku cewa, mun samu matsala a tsarin yau 07 ga Nuwamba 2024 da ƙarfe 11:29 na sa’o’i wanda ya shafi wadata a cikin hanyar sadarwarmu,” Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ikeja (EKEDC) da ke aiki a sassan Legas ya rubuta a shafinsa na Tuwita.
“Ana ci gaba da kawo kayan aiki tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsakinmu.
Ku yi haƙuri da mu.”
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko (EKEDP) ya kuma sanar da abokan cinikinsa game da “ɗaukewar lantarkin.
“A ln sanar da mu cewa a daidai sa’o’i 11: 29 a yau, 7 ga Nuwamba, 2024, mun samu asarar wadatar kayayyaki a lokaci guda a faɗin hanyar sadarwar mu,” in ji EKEDP.
“A na zargin yuwuwar gazawar tsarin ko rugujewa. A halin yanzu muna aiki tare da abokan aikinmu kamar yadda mu ke fatan sake dawo da babban layin cikin sauri.”
A ranar Talata wasu sassa na Nijeriya sun shiga cikin duhu bayan da layin wutar ya ruguje. Miliyoyin gidaje ba su da wutar lantarki kuma suna jiran cikakken maido da tsarin.
