Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bayan da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin su a ranar Litinin, wasu yara ƙanana, masu shekaru tsakanin 14 zuwa 17, da aka kama a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa a faɗin ƙasar a watan Agusta, sun bayyana abubuwan da suka fuskanta a yayin da suke tsare.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai babban sufetan ‘yan sandan ya gurfanar da mutane 76 da suka haɗa da yara ƙanana 32 waɗanda aka kama yayin zanga-zangar, bisa laifuka 10 da suka shafi cin amanar ƙasa, da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya da kuma tada zaune tsaye ta hanyar yin kira ga sojoji da su karɓe ragamar mulkin ƙasar daga hannun gwamnatin Shugaba Tinubu, da dai sauransu.
Huɗu daga cikin yaran da ake ganin kamar ba su da isasshen ƙoci, sun faɗi ƙasa warwas ne a yayin zaman kotun da ke gaban mai shari’a Obiora Egwuatu a sashin Abuja na babbar kotun tarayya.
Hakan dai ya janyo cece-kuce a faɗin ƙasar, inda ƙungiyoyin farar hula da masu rajin kare haƙƙin jama’a ke zargin ’yan sanda da gwamnati kan yadda suka gallaza wa ƙananan yaran, waɗanda suke daga jihohin Kano da Kaduna.
Bayan hayaniyar, Ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Mohammed Idris, a yayin wani taron gaggawa da aka yi a ranar Litinin, ya shaida wa manema labarai na fadar shugaban ƙasa cewa, shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta sakin yaran.
Don haka, babbar kotun Abuja da ke Abuja ta yi watsi da tuhumar da ‘yan sanda suka yi wa masu zanga-zangar.
Waɗanda suka fito daga Kano dai an ajiye su a Asibitin kwararru na Muhammadu Buhari, inda tawagar ma’aikatan lafiya ke duba su da kuma kula da su. Ana sa ran za su ci gaba da zama a asibitin na tsawon kwanaki biyar, kafin a haɗa su da iyalansu.
Wasu daga cikinsu da suka zanta da manema labarai a asibitin ƙwararru na Muhammadu Buhari inda aka kai su Kano a daren ranar Talata, sun ce jami’an gwamnati sun hana su abinci na tsawon kwanaki.
“Mun hango lahira ɓaro-ɓaro; mun sha wahala sosai,” in ji ɗaya daga cikin yaran mai suna Umar Ali, mai shekaru 15.
“Wani lokaci muna kwana uku ba abinci. Kuma ko da an ba mu abinci, ba ya wadatar da mu.”
Ali ya musanta cewa yana da hannu a zanga-zangar inda ya ce an kama shi ne a hanyarsa ta zuwa kasuwa a Kwana Hudu da ke ƙaramar hukumar Ungoggo a jihar, inda ya kan yi ayyukan buga-bugan sa domin samun na abinci.
Ya ƙara da cewa, an ajiye su a cikin duhu lokacin da ake tsare da su, wanda ya ce ya shafi wasu daga cikinsu a lokacin da aka kai su kotu.
“Da kyar muka ga hasken rana a wurin da aka ajiye mu, dalilin da ya sa wasun mu ba su iya gani sosai a lokacin da aka kawo mu kotu,” inji shi.
Wani matashi mai suna Ibrahim Aliyu Musa, wanda aka ɗauke shi daga Kano zuwa Abuja kwana guda bayan kama shi, ya ce an ajiye shi tare da wasu gawurtattun masu aikata laifuka.
“Ina cikin waɗanda aka ajiye a wuri guda tare da masu laifi kuma a wasu lokuta muna shafe kwanaki da yawa ba tare da abinci ba.
“Abincin ba wani abu bane mai yawa, babu isasshe kuma babu ɗanɗano. Suna kawo mana wake da safe, shinkafa da rana, Gabza kuwa abincin dare. Ana shirya Gabza ga fursunoni saboda yawansu. Don haka sai da muka ci Gabza domin mu rayu,” in ji Musa.
Shi ma da yake ba da labarin abin da ya faru da shi, wani yaro ɗan shekara 13, wanda ya ce an kama shi ne a Gadon ƙaya da ke ƙaramar hukumar Gwale, ya ce ana tuhumar sa ne da ɗaga tutar ƙasar Rasha, wanda ya musanta aikata hakan.
“An kama ni ne a ranar 15 ga Agusta, kuma washegari aka kai ni Abuja. An ajiye mu a Abattoir SARS da ke Abuja. An tsare mu tare da masu laifi tsawon kwanakin da muka yi a wurin,” inji shi.
Masu zanga-zangar 39 da aka tsare daga jihar Kaduna a ranar Laraba sun sake haɗuwa da iyalansu.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya bai wa yaran da aka saki kyautar manyan wayoyi da kuɗi kimanin naira 100,000.
Gwamnan ya kuma alƙawarta bai wa mutum 39 ‘yan jihar da aka saka – horo domin sake musu tunani, tare da ba su jari, idan sun kammala samun horon.
Sakataren gwamnatin jihar, Abdulkadir Meyere ne ya bayyana haka.
Ya ƙara da cewa, gwamnan jihar ya bayar da umarnin da ya karɓi takardun matasan da suka kammala karatu a cikinsu.
“Gwamna ya alƙawarta cewa za a bayar da jari ga wasunsu domin su fara sana’a, yayin da za a koya wasu sana’o’in wasu kuma gwamnati za ta ɗauke su aiki,” in ji shi.
