Daga IBRAHIM MUHAMMAD
Wata ƙungiyar ta matasa mai suna ‘APC Arewa Youths Merger Group’ ta yaba wa shugaban ƙasa Ahmad Bola Tunubu bisa karɓar ƙorafinsu da kira da suka yi masa akan ya sa a saki yara da aka tsare akan zanga-zanga cikin awa 48.
A cikin wata takardar sanarwa dake ɗauke da sa hannun jagoran Matasa na APC Arewa merger group Hon Musa Mujahid Zantawa aka raba wa manema labarai yace sun yi matuƙar jin daɗi da farin ciki da yafe wa yaran da shugaban ƙasa ya yi bayan amsa kira da sukayi masa ya kuma miƙa su hannun gwamnonin jihohinsu wanda dama haƙƙin gwamnonin ne su yi ƙoƙarin karɓo su amma suka kasa aiwatarwa da haka ne.
Ya yi nuni da cewa musamman ma gwamnan jihar Kano da mafi yawan yaran ’yan asalin Kano ne kuma shi ne ma ya bai wa Kwamishinan Shari’a na jihar tun farko umurnin a kai yaran kotu a hukunta su amma ake nema a sa siyasa a maganar, dole ne yanzu Gwamnatin Kano ta fito ta nemi gafarar waɗannan yara da a dalilin matakin da ta ɗauka ne suka shiga wannan yanayi.
APC Arewa Youths Merger Group ta ce a lokacin da suka kaiwa yaran ziyara a inda ake tsare dasu sun kai musu tallafi na kayan abinci dana buƙatun yau da kullum, sun yi musu alƙawari dama a cikin awanni 48 za su nemi alfarma wajen shugaban ƙasa ya sa a sake su, kuma sun nema, shugaban ƙasa ya amsa kiran nasu ya sa aka sake su.
Hon. Musa Mujahid Zantawa ya ƙara jaddada godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunubu a madadin matasan APC akan wannan shawara tasu daya ɗauka hakan ya tabbatar da cewa shi ɗan Damakwaraɗiyya ne ,sannan suna kara kira a gare shi ya dauki nauyin karatun waɗannan yara da aka saki domin su zama masu kyakkyawar makoma nan gaba idan suka zama masu ilimi.
