Daga MUHAMMADU MUJJITABA A KANO
Ƙungiyar Mata Teloli ƙarƙashin shugabancin Hauwa’u Dauda Ibrahim, da Rahinatu Umar Yahaya, sai Hafsa Adam Abubakar, da sauran shugabanin ƙungiyar 15 wacce ta ke da shugabani 18 kenan ta gabatar da gagarumin taro karo na farko da inganta sana’ar ɗinki a tsakanin al’umma a Kano.
Wannan taro shi ne irinsa na farko kamar yadda shugabanin wannan ƙungiya mai sana Kanawa Zumata Tailoring Multi Coropritiɓe Serɓerse suka tabbatar a wannan taro a jawabansu daban-daban a taron da suka gabatar a ƙarshen mako a ɗakin taro na gidan tunawa da marigayi Malam Amimu Kano, da ke unguwar gwammaja Kano.
A jawabinta Hajiya Hauwa’u Dauda Ibrahim, ta ce shekaru 18 tana wannan sana’a kuma sana’a ce mai albarka musamam irin yadda suke taimakawa harkokin gida na yau da kullum wajen farantawa mazajensu ba dan sun gaza ba, kuma akwai buƙatar ko wacce mace ta tabbatar ta na da sana’a komai wadatar mai gidanta Allah ne kawai baya buƙatar taimakon wani bawansa amma bawa na buƙatar taimako daga mahalici.
Kuma abunda suka kiyaye shi ne cika alƙawari a wannan sana’a kuma basa cikin teloli masu yin ɗinki da ya saɓa al’ada ko addini musamam kasancewa wannan jaha ta al`umma ce masu riƙo da adini da ƙaunar ma’aikin Allah.
Ita kuwa Rahinatu Umar, ta tabbatar da cewa kaƙasudin wannan taro shi ne warware matsalokin da ke damunsu a wannan sana’a ta yadda aka gayatu masu ruwa da tsaki a harkar ɗinki kamar masu sayar da yadi da masu sayar da zare da sauransu inda ake samun ƙaranci ko tsada a wasu kayayyaki da nufin magance matsalolin da ake samu a lokacin ɗinki inda sukeyi wanda yana taimakawa da inganta rayuwarsu da iyalansu.
A ƙarshe ita ma ɗaya daga cikin shugabanin ƙungiyar Telolin ta Kanawa Zamuta Tailoring Multicoropritiɓe serɓices Hafsatu Adam Abubakar, ta ce wannan sana’a ta tayi mata 19 ta arziƙi domun taje Umara da abunda ta samu a wannan sana’a dan haka babban ƙalu bale ne ga yan uwa mata na cewa sana’ar ɗinki babbar sana’a ce da ta ke da rufin asiri mudun mai yenta zai kula da ƙa’idojin aiki tsakani da Allah ta hanyar tsayawa akan gaskiya kamar yadda ko wacce sana’a ko mu’amula ta ke buƙata, inda ɗaukacin shugabanin wannan ƙungiya ta Teloli sukayi kira ga gwamnati ta kawo musu taimako ta yadda zasu samu saukin hurar da yan uwansu mata masu buƙatar koyar wannan sana’a ta ɗinki.
