Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
A matsayina na marubuci mai bincike, ba na goyon bayan wata siyasa ko wani ɗan siyasa. Haƙƙinmu shi ne bincike da lalubo gaskiya daidai fahimtarmu domin bayyana wa al’umma ko Allah zai sa a sami gyara cikin al’amuran zamantakewar mu.
A yan kwanakin nan hazon siyasar Kano ya yamutse sakamakon rikice-rikice cikin jam’iyyar NNPP da kungiyar Kwankwasiyya. Kafin na tsunduma kan maudu’in, akwai bukatar mu koma baya mu duba tarihi.
Idan bera da sata, to daddawa ma fa akwai wari. Wato idan ka kalli siyasar Kwankwaso tun daga shekarun 1990 zuwa yanzu zaka samu cewa ya fandarewa masu gidansa irinsu Abubakar Rimi, Senator Hamisu Musa, Musa Gwadabe, Lili Gabari, tare da raba gari da abokai ko yaransa a siyasa irinsu Ganduje, Nasiru Aliko, Rabiu Suleiman Bichi, Dangwani, Ado Doguwa, Kawu Sumaila, Barau Jibrin, Abdulmumini Jibrin, har da Ma’aikata irinsu marigayi Umar Said Tudun Wada wanda ya ajiyewa Kwankwaso aikinsa na Director Media, da sauransu.
Siyasar Najeriya, musamman a Arewa ta gaji irin wannan domin kafin Kwankwaso mun ga yadda shi kansa Abubakar Rimi ya fandarewa Malam Aminu Kano. Da yadda ta kasance tsakanin Obasanjo da Atiku, ko a nan kusa tsakanin Obaseki da Mataimakinsa, Nasiru El Rufai da wanda ya gaje shi.
A wannan satin bidiyon Ali Madaki ya karade kafofin sadarwa inda cikin fushi ya ke korafe-korafe a kan Madugu. Wasu da dama na hanzarin ganin laifin Madaki da kiransa Butulu ko mahassadi. To kamar yadda na fada a baya dama siyasarmu ta gaji butulcin, sannan ana cewa ya manta da alherin da Kwankwaso ya yi masa. Babu wani Dan siyasa a Kano da ya ci moriyar Kwankwaso irin Ganduje, amma ku duba yadda su ka zama, kuma har zuwa yanzu Ganduje na azabtar da Kwankwaso da Kano sakamakon wannan gaba.
Idan an bi ta barawo, to lallai a bi ta mabi sahu. Ali Madaki ya fara siyasa ba a karkashin Kwankwasiyya ba, sannan ni shaida ne na irin nasa halarcin da ya yiwa Kwankwaso. Domin a 2018 na sami labari na sirri cewa su Nasiru Aliko da wasu shugabanni a Dala bisa umarnin Ganduje su na yunkuri lallai sai sun hana Ali Madaki komawa kan kujerarsa ta Dan Majalisa, saboda sabon rikicin da ya balle na Kwankwasiyya-Gandujiyya. A wannan lokaci, duk yadda ka kai da adawa da Madaki, dole ka cira masa tuta a matsayin Dan Arewa tilo da ke tsaye wajen kare muradan yankin Arewa da Musulmi. Kuma a Sani na, tun daga 1999 zuwa yau bamu taba samun Dan Majalisa a Dala da zaka iya tunkahon cewa ba mai dumama kujera ba ne. Duk da cewa a Dala, mutane na korafin rashin jan Yan jam’iyya da talakawa a jiki. Ni kaina Ina da nawa korafi a kansa.
Amma Kasancewar abokina ne na tsawon shekaru tun kafin a shiga siyasa, wancan labari ya daga min hankali, musamman idan na yi la’akari da cewar Babangida Yakudima ake son a maye gurbinsa da shi. Domin na tabbatar Babangida ba shi da rabi-rabin capacity din Madaki. Don haka sai na nemi Madaki na gaya masa ga irin shirin da ake yi kuma hakan zai janyo mana asarar babbar murya, ba ta Dala da Kano kadai ba har ma Arewa. Madaki ya yarda da sahihancin labarina, sanin cewa a baya na taba yiwa Nasiru Aliko PA sanda yana National Youth Leader na PDP. Ya yi min godiya saboda nuna kulawa ta a gare shi, amma saboda ka san mai taurin kai ne (sunan namu sai a hankali) sai ya kekasa kasa ya min rantsuwar cewa wallahi da ya bi su Ganduje ya bar Kwankwaso, gara ya rasa kujerarsa ta Majalisa. Wannan bayani nasa ya matukar bata min rai saboda na hakkake a cikin raina zai rasa kujerar kuma ya cuci constituency dinsa.
Na rabu da shi kuma a karshe aka maye gurbinsa da Babangida Yakudima wanda ya lashe kujerar. A zuciyata na hakkake wata rana sai Madaki ya yi da-na-sanin wannan lamarin. Da aka zo zaben 2023, Madaki ya yi kokarin a bashi takarar Senatan Kano ta tsakiya, kuma da farko kamar Kwankwaso zai ba shi, amma zuwan Shekarau ya danne tasa bukatar. Tafiyar Kwankwaso da Shekarau ba ta yi karko ba don haka Shekarau ya yi watsi da takarar ya fice daga jam’iyyar. A mutunce kamata ya yi a tabbatarwa Madaki da wannan takara ta senator, amma kamar yadda zargi ya nuna sai aka siyar da takarar.
Don haka ban yi mamaki ba kwata-kwata, ganin yadda Madaki ya fito ya na babatu a kan Madugu da Kwankwasiyya, abu ne da na ke jiran gani. Duk wanda ya kai tsaiko a wajen Kwankwaso babu wanda ba su raba gari ba. Me hakan ke nunawa? Dole Kwankwaso ya canza tsari kafin lokaci ya kure masa. Hatta Gwamna Abba, idan bai yi taka tsantsan ba, wallahi sai sun raba gari. Kuskure da mutane ke yi shine zaton zaka iya juya yaronka dari bisa dari bayan ya sami mulki. A’a, kuskure ne, wallahi ko Dan cikinka idan baka bi a hankali ba zai iya keta muradinka idan ya sami mulki.
A bayyane ya ke cewa katsalandan da Kwankwaso ke yi tun kafa wannan gwamnati, shi ya hana ta tsinana abin azo a gani yadda da yawanmu muka tsammata. Gwamnatin ta shigo da fushin Kwankwaso aka kama rusau mara ma’ana domin kuntatawa wasu. Rigimar kotu ta tsaida komai sannan ana samun nasara ta ba zata, maimakon a yi shukara a kama aiki sai aka dauko matsalar masarauta wadda ya kamata a ce an wuce wurin saboda kwadayi irin na masu sarauta. Yau an wayi gari da Sarki biyu a kano, to, wa gari ya waya? Kwadayin masarautan ya sa da hannunsu sun rusa masarautar tasu da kansu. Akwai tarin matsaloli na al’umma musamman talauci da Yunwa da gwamnatin Tinubu ta haifar, kuma Kano ba ta taba samun kudade irin wannan dan tsukuku ba daga gwamnatin tarayya amma ba wani hobbasa na a zo a gani wajen bunkasa harkar noman abinci da samar da ayyuka GA matasa.
Kano na da Dams 22 su na barci. Ba za ku gane mahimmancin wannan Dams ba sai kun gane cewa Dam din Tiga, wanda kaso 40% kacal ake amfana tsawon shekaru 50, ya sa kananan hukumomin Rano, Bunkure, Kura, Garun Malam, Tudun Wada da Doguwa sun kasance yanki mafi albarkar noma a yankin Arewa. Sannan saboda noman rani tsawon shekara, ko Almajirai na wannan yanki baka gani.
Wannan albarka ta dams 22 a Kano ya sa na yi binciken yanayi (feasibility Studies) na tsawon kusan shekara yadda za a amfane su ta hanyoyi da dama. Kai har kamfani a China na samo wanda ya nuna sha’awar zuwa ya zuba jari akai. Ni da Hamisu Iyantama mun je mun sami kwamishinan albarkatun ruwa, Hon Ali Makoda, na yi masa power point presentation kuma kamar ya rungume mu saboda ganin mahimmancin abin, da irin kudaden shiga da zai samawa Jihar Kano . Ya shawarce ni da na rubuta takarda ga mai girma Gwamna na neman a bani dama na je gaban majalisar gudanarwa ta jiha na yi musu wannan presentation. Sannan ya ce zai tattaro directors dinsa mu zauna a yi musu presentation a sati na gaba domin su bada shawarwari. Na rubuta takardar na kai ofishin Gwamna an karba, amma yau wata biyar kenan, Ali Makoda ya daina daukar waya, kuma takardar na ofishin Gwamna shiru kake ji, Malam ya ci shaho.
Yaushe za mu tattaru wajen hada hannu domin ganin mun ciyar da jiharmu gaba don Allah. A duk wata fa ana haihuwar mutane sabbi kimanin 27,000 a Kano, nan da shekaru 30 zamu fi akasarin kasashen Afirka yawan jama’a. Idan ba mu yi tanadi a kan ilimi, noma da ayyuka yi ba, wallahi masifun da zamu barwa yayanmu, sai Boko Haram, banditry da kidnap sun zama kauyanci. Allah ya hore mana komai a Kano: yawan jama’a, dam-dam, koramu, kasar noma da masu ilimi. Ya kamata don Allah Kwankwaso ya tattaro mutanensa wajen guda a karkata hankalin gwamnati wajen samarwa da rarraba arzikin Jihar. Lokacinsa da na gwamnatin duk ya kusa kurewa, kuma ya sani Rimi da Audu Bako ba su mutu ba, ba domin komai ba sai saboda kullum ana kallon gudunmuwarsu mai dorewa da su ka bari, yadda har a nade Kano, Kanawa za su dawwama cikin yi musu addua. Madugu ya kamata ka biyo jerin wadannan gwaraza da tarihi ba zai taba mantawa da su ba.
