Hanyoyin magance matsalar tsadar rayuwa

Spread the love

Daga  HASSAN IMRAN 

Masu iya magana su na cewa, ‘Ba a gayawa mahaukaci ana ruwa; in ruwan ya dake shi zai sani.’ Babu wanda bai san matsalar da ake fuskanta a ƙasar nan ta tsadar rayuwa ba. Kowa na ji a jinkinsa! Wannan tsadar rayuwa na ɗaya daga cikin matsalar da ta addabi duniya gabaɗaya, amma a fuskokin da ta bambanta. Kayan masarufi da kayan abinci sun yi hauhawar da ta wuce lissafi. 

Wannan tsadar rayuwa ba iya birnin kaɗai ta taƙaita ba, hatta mutanen n karkara na jin zafin ta. Masana sun yi bayani cewa musababin wannan tsadar rayuwa shi ne taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasa, faɗuwar darajar Naira a kasuwannin musayen kuɗaɗe na duniya, da kuma janye tallafin mai fetur. 

A yau, biredin da ake sayar da shi ₦350 a shekarar 2020 ya koma ₦1,500. ƙwai da a ke sayar da shi ₦20 a wasu shekarun baya ya koma ₦300, a wasu wuraren ma har ₦350 ne. Haka zalika, kuɗin hawan jirgin sama, magunguna, kuɗin hayar gidaje, makamashi irinsu man dizul, gas din girki, buhun shinkafa, naman kaza da na talo-talo da sauran muhimman kayayyakin duk sun yi tashin gwauron zabi. Amma abin takaici, albashi ko kuɗin da ke shigowa ta hanyar kasuwanci bai ƙaru ba, a wajen wasu ma raguwa ya yi. Babu abinda ke da sauƙin saye. Komai ya gagari talaka. 

La’akari da wannan yanayin da muka samu kawunanmu a wannan ƙasar, da kuma rashin kyakkyawan ƙarin albashin ma’aikata; ya janyo rashin ajiya ko kuwa tanadin kuɗaɗe, domin buƙatun yau da kullum. ƙuncin rayuwa, takaici da baƙinciki, saurin fushi da kuma rashin iya ɗaukar dawainiyar gida.

Tsadar rayuwa ta janyo matsaloli da yawa da suka yi tasirin a kan talakawa ta fanni ƙwaƙwalwarsu, zukatansu da kuma lafiyar jikinsu, don hatta zamantakewar aure da kuma hanyoyin samun su na kullu yaumin. A yanzu, ko da albashi mutum ana biyan shi akai akai, rayuwa ta yi tsada fiye da tunanin mutum. A kullum, farashin yau ya bambanta da na jiya. Haka al’umma ke rayuwa a wannan matsatsin yanayi. 

Saboda haka, bunƙasa hanyoyin samun kuɗi ta hanyar halak tana ɗaya daga hanyoyin da za su kuɓutar da mutum a wannan yanayin tsadar rayuwa. Bugu da ƙari a kan albashi da ribar kasuwanci, yana da kyau mutum ya nemi wata sana’ar da wasu ayyukar na gefe da za su taimakawa mutum a wannan yanayin da ake cikin. Akwai hanyoyin samun kuɗi da yawa ta manhajar yanar gizo irin su tallace-tallacen zamani ta shafukan sada zumunta (Digital marketing), koyarwa ta shafukan sadarwa irin su Zoom, Google Classroom da sauran su. Haka zalika, ƙaddamar da nasiha ko muhadara a taro ko bukukuwa (Guest Lecturing),  da kuma juya wata baiwa ko fasaha ta hanyar samun shi ma na daga cikin hanyoyin da za su kuɓutar da mutum a wannan yanayin da muke ciki. Gina gidaje domin ba da haya, da kuma siyan filaye na daga cikin hanyoyin bunƙasa arziƙi. 

A nawa la’akari, da yawa daga cikin mutane da kuma magidanta sun fi dogara ne akan albashi wasu kuma sun dogaro ne akan ribar kasuwanci na yau da kullum, kuma fatansu shi ne rayuwa ta canza ko ɗan kaɗan ne. Irin wannan tunanin, a duk lokacin da rayuwa ta canza halinta yana haifar da matsalar ciwon ƙwaƙwalwa, yawan ƙunci da damuwa, wahalhalu da tsoro. Ala kulli halin, mu sani cewa bunƙasa hanyoyin samun mu ita ce mafita da za mu kare kanmu, da iyalanmu da harkokin kasuwancinmu daga barazanar lalacewar tattalin arziƙi. 

A ƙarshe, gwamnati ta sauya tsare-tsarenta na tattalin arziƙin ƙasa da za su sauƙaƙa wa al’umma rayuwarsu. Masu hannu da shuni su taimaka wa marasa galihu da kayan abinci domin ragewa talakawa wannan ƙuncin rayuwa da ake ciki.

*Hassan Imran ya aiko da wannan nasiha ne daga Jos, Babban Birnin Jihar Filato, kuma za a iya samun sa kan addreshinsa ta yanar gizo [email protected]

By ukarofi