Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI
Abubuwa uku da ke inganta lafiyar kayan cikin mutum
1. Ruwa:
Shan isasshen ruwa, kamar yadda na sha faɗa , na da tasiri ga lafiya sosai. Isasshen ruwa yana bawa kayan cikin damar aikata ayyukansu cikin nutsuwa irinsu narka abinci da kuma rashin gazawa da wuri.
2. Kayan marmari
Tuffa, Gwanda, kankana da sauransu su ma ba zan barsu a baya ba. Dan akwai nazari da masana suka nuna cewa ƙarancin shan kayan marmari na jefa mutum haɗarin samun kansar tumbi.
3. Azumi
Na yi ‘series’ na rubutu akan tagomashin da azumi ke ba wa jikin ɗan adam. A ɓangare na lafiyar kayan ciki, azumi na kore datti da cututtuka da ke makalewa a lungu da saƙon da ke cikin hanyoyin da abinda ka ci ya ke bi ya wuce.
A yayin azumi, kayan ciki irin su tumbi da ’ya’yan hanji na takurewa su ingizo wani ‘vibration’ da ke share duk wani abu da ya maƙale.
Saboda haka a kula da waɗannan abubuwa uku, domin inganta lafiyar cikinku. Shan isasshen ruwa a kowacce rana, yawan shan kayan marmari da ganyayyaki da kuma azumi.
Naku MIAbdullahi
