Tinubu ya dawo Abuja daga taron Saudiyya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar kwana guda da ya kai Riyadh a Saudiyya domin halartar taron gaggawa na ƙasashen Larabawa da Musulunci da aka kammala kwanan nan. Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja da misalin ƙarfe takwas na yammacin ranar Talata.

A wurin tarbar shugaban ƙasa, akwai shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da shugabannin tsaro da wasu ministoci, ciki har da Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya, da Wale Edun, Ministan Kuɗi da Tattalin Arziki.

Haka zalika, Shugaban Jam’iyyar APC mai mulki, Abdullahi Ganduje, ya kasance a wajen don tarbar shugaban ƙasa.

Taron wanda Sarki Salman da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman suka shirya, ya mai da hankali kan muhimman batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya.

Yayin da yake gabatar da jawabinsa a taron, Tinubu ya yi tsokaci kan rikicin Isra’ila da Falasɗinu, inda ya yi kira da babbar murya kan a gaggauta tsagaita wuta tare da samun mafita mai ɗorewa cikin lumana.

By ukarofi