Lakurawa: Daga sojojin haya zuwa ‘yan ta’adda

Spread the love

Asalin Lakurawa da alaƙarsu Al-qa’eda

Gaskiyar magana kan harin Mera da abinda ya biyo baya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja da JAMIL GULMA a Birnin Kebbi

Lakurawa, kamar yadda ake kiran ayarin waɗansu mutane da ke da’awar Musulunci tsantsa da suke da sansanoni akan iyakokin Tarayyar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar tun daga yankunan ƙananan hukumomin Arewa da Augie da ke Jihar Kebbi zuwa ƙananan hukumomin Gudu da Tangaza da Silame da Kware da Gwadabawa zuwa Illela da ke Jihar Sokoto, mutanen da ke zaune a waɗannan yankunan sun daɗe suna ganin waɗannan mutanen ɗauke da makamai suna shiga garuruwansu suna sayayya musamman kayan abinci da sauran kayan masarufi na amfanin yau da kullum.

Waɗannan mutanen kamar yadda Wakilin Blueprint Manhaja ya bankaɗo ya nuna gamin gambiza ne da akasarinsu matasa ne masu jini a jika da suka haɗa da Fulani da Buzaye da Larabawa da suka fito daga ƙasashen Tarayyar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da Mali da Libiya da Sudan da sauran ƙasashen Afrika da mafi yawancin suna magana ne da yaren Fulatanci da Larabci da kuma Faransanci kuma suna sanye da tufafin sojoji.

Suna yin da’awar Musulunci ne kuma suna yin rangadi kan manyan babura a waɗannan yankunan suna da’awar karɓar haraji ko kuma zakka ta dabbobi daga Fulani da kuma mutanen gari da suka mallaki dabbobi masu yawa.

Wakilan Blueprint Manhaja a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya da Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar Kebbi, SANI AHMAD GIWA da JAMIL GULMA, sun shirya mana rahoto na musamman kan wannan ƙungiya ta Lakurawa, wacce Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ayyana a matsayin ta ’yan ta’adda kwanan nan.

Asalin Lakurawa:

Wani bincike da aka yi a shekarar 2021 ya nuna cewa, ƙungiyar Lakurawa ta shigo Nijeriya ne bayan goron gayyatar da shugabannin gargajiya a ƙananan hukumomin Gudu da Tangaza da ke jihar Sakkwato suka yi musu a shekarar 2017 biyo bayan barazanar ‘yan bindiga daga jihar Zamfara.

Rundunar Sojojin Nijeriya na kallon Lakurawa ne a matsayin wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci da ta shigo a jihohin Sakkwato da Kebbi daga ƙasar Nijar bayan juyin mulki.

Sai dai Blueprint Manhaja ta gano cewa, Lakurawa na da alaƙa da ƙungiyar Al-ƙaeda kuma tun kafin juyin mulkin ƙasar Nijar akwai wannan ƙungiya.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata, Rundunar Sojin Nijeriya ta ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ƙungiyar ta’addanci da ke ayyukan ta’addancin a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Ta bakin mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya ce, ƙungiyar Lakurawa na da alaƙa ne da ’yan ta’adda da ke yankin Sahel, musamman ƙasashen Mali da Nijar. Manjo Janar Buba ya ce, Lakurawa sun fito ne daga Mali bayan yankewar alaƙar Nijeriya da Nijar a kwanakin baya.

Alaƙar Lakurawa da Al-ƙa’eda:

Tun bayan ɓullar wannan ƙungiya ta Lakurawa ake ta shaci faɗin daga ina suka ɓullo kuma su wane ne su. Wasu na alaƙanta su da wata babbar ƙungiyar ta’addanci da ke yankin Sahel  mai taken ISGS, sai dai akwai wani bincike da ya nuna hakan ba gaskiya ba ne.

A binciken da Murtala Rufa’i, James Barnett da Abdulaziz Abdulaziz suka yi a shekarar 2022, ya nuna cewa, Lakurawa sun ƙi amincewa da a kira su da sunan Boko Haram, sai dai a kira su da sunayen Mujahideen ko Ansaru, waɗanda sunaye ne da ake kiran ƙungiyar al-ƙaeda da su.

Kamar Lakurawa, ƙungiyar Ansaru ta yi wa al’ummar da ta ke zaune a cikinsu alƙawarin ba su kariya, inda suke kai wa jami’an tsaro hari da kuma fararen wutar da take wa kallon ’yan leƙen asiri ne ko kafirai. ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru tana da tsarin tunani ne irin na Lakurawa, wacce ake yi amanna cewa su ne suke ayyukan ta’addanci a Jihar Kaduna, musamman ma a yankin Birnin Gwari. Wannan dai na nuna cewa, masu iƙirarin jahadi sun fara maye gurbin ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.

Masu binciken sun alaƙanta Lakurawa da ƙungiyar Jama’at Nusrat Al-Islam Wal-Muslimin (JNIM), wacce ita ma reshe ce ta Al-ƙaeda da ke ƙasar Mali kuma an kafa ta ne a shekarar 2017 a lokacin da wasu ƙungiyoyin ta’addanci suka yi haɗaka. ƙungiyoyin su ne: Ansar al-Din, al-Murabitun, Macina Liberation Front (MLF) da Sahara Emirate Subgroup ta al-ƙa’eda.

Daga sojojin haya zuwa ‘yan ta’adda:

A cewar binciken masanin tarihin ayyukan ta’addanci, Mista Rufa’i, ya bayyana, an gayyato ƙungiyar ne zuwa yankin Sakkwato a shekarar 2017. Wannan ya biyo bayan kai hare-hare da ’yan bindiga ke tsallakewa daga yankin Jihar Zamfara zuwa ƙauyukan Jina-Jini, Wassaniya, Tabaringa da Mulawa da ke ƙananan hukumomin Tangaza da Gudu. Haka kuma ’yan bindigar na addabar gabashin Sakkwato kamar ƙauyukan Isa, Sabon Birni, Raɓah, Goronyo da Illela.

Mista Rufa’i ya ce, “Lukurawa sun fara ne da adadin da ba su wuce 50 ba, amma a hankali suka yi ta ƙaruwa har zuwa su 200 kuma mafi yawa yaran matasa ne daga shekara 18 zuwa 35.

A cewar wani shugaban gargajiya na ƙauyen Balle da ke ƙaramar Hukumar Gudu kuma, mutanen Mali ne da ke magana da yaren Arabiyya ko Fulfulɗe.

Dagacin garin Balle na ƙaramar Hukumar Gudu ya ce, tare da shi da Dagacin Gongono da ke ƙaramar Hukumar Tangaza sun zauna da Alhaji Bello Wamakko, wanda shi ne Shugaban ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah a wancan lokacin, inda suka tattauna A kan yadda za a ɓullo wa waɗannan ’yan bindigar Zamfara. Daga ƙarshe suka yanke shawarar ɗaukar hayar Lakurawa daga Mali domin magance mana ‘yan bindigar.

“Wannan shi ne yunƙurin farko wanda da aka yi duk da cewa na gargaɗi gwamnan kan gayyatar waɗannan mutane,” inji shi.

Kenan waɗanda suka gayyato su suna da kamasho game da laifin ba su dama da har suka bunƙasa.

Lakurawan kan nemi tallafi na kuɗi ko na shanu ko na ababen hawa da makamai.

A lokacin da kafafen yaɗa labarai suka bayyana kutsen Lakurawa a shekarar 2018, ’yan sanda sun ƙaryata labarin, inda suka ce makiyaya ne kuma ba su da makamai da suka kawo dabbobinsu kiwo.

Lakurawa sun fara ta’asa ne bayan kashe Dagacin garin Tangaza, wanda yana guda daga cikin waɗanda suka gayyato su, inda suka zargi ɗan mamacin da hannu kan riƙe musu kuɗinsu da ya kai Naira miliyan 63. Daga baya ne suka kashe shi, saboda musanta zargin da suke yi wa ɗansa.

Kuma kafin faruwar wannan al’amari, Lakurawa sun ta yi wa mutane wa’azi tare da karɓar zakkar dabbobi daga makiyaya kamar yadda wani jagoran matasa, Bashiru Tagimba, ya bayyana wa Rufa’i. Sannan sukan duba wayoyin mutane tare da fasa memori ɗin da ke ɗauke da waƙa.

Sakamakon damun jami’an tsaron Nijar da hare-hare ya sa rundunar sojin Nijar haɗa kai da ta Nijeriya wajen yaƙar waɗannan mutane a 2018. Kuma mafi yawa daga cikin malamai da sarakunan gargajiya sun dawo daga rakiyarsu a lokacin da suka kauce hanya daga dalilin gayyato su.

Sai dai Blueprint Manhaja ta gano cewa, rashin bai wa manema labarai dama ne ya sa al’umma ba su san da su ba. Kuma saboda gazawar mahukunta ne Lakurawan suka sake haɗa kansu a 2021 tare da kai wa ’yan bijilanti hare-hare. Haka kuma yanke alaƙar sojoji da Nijeriya da Nijar suka yi, saboda juyin mulki, ya ƙara ta’azzara wannan al’amari na Lakurawa a yankin Sakkwato.

Yadda Lakurawa ke neman abokan aiki a kafar sada zumunta – Hedkwatar Tsaro:

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce, sabuwar ta’addanci ta Lukarawa ta fara aikin ɗaukar ma’aikata ta hanyar kafafen sada zumunta na zamani, domin ƙara ƙarfi da faɗaɗa ayyukansu.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, Hedkwatar Tsaro, duk da haka, ta ce, sojojin na sane da ayyukan ɗaukar ma’aikata na ƙungiyar tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro da gwamnatin jiha domin dakatar da yunƙurin ɗaukar ma’aikatan.

Hedkwatar Tsaro, a ranar Alhamis ɗin makon jiya ta tabbatar da ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ta’addanci da aka fi sani da ‘Lukarawa’ a yankin Arewa, tare da gudanar da ayyukanta a jihohin Sakkwato da Kebbi.

Daraktan Yaɗa Labarai, Manjo Janar Edward Buba, ya ce ‘yan ta’addan sun fara kutsawa cikin yankunan arewacin jihohin Sakkwato da Kebbi daga jamhuriyar Nijar da Mali, musamman bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar. Ya zargi mazauna yankin da karɓar ‘yan ta’addan da kuma kasa kai rahoton duk wani motsi nasu ga sojoji da sauran jami’an tsaro.

A ranar Juma’a ne sabuwar ƙungiyar ta’addancin ta kai hari a garin Mera da ke ƙaramar hukumar Augie a jihar Kebbi a daidai lokacin da jama’ar yankin ke shirin gudanar da sallar Juma’a, inda suka kashe aƙalla mutane 15 tare da kwashe shanu aƙalla 100.

Yayin da yake magana da Wakilin Blueprint Manhaja a ranar Talata, Janar Buba ya ce, ’yan ta’addan na amfani da wa’azi da jan ra’ayin jama’a wajen yaudarar matasa. Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta’addancin na kuma amfani da kafafen sada zumunta wajen gudanar da ayyukanta na ɗaukar ma’aikata.

Buba ya ce, “ƙungiyar tana amfani da kafafen sada zumunta na zamani, tana wa’azi da jan hankalin jama’a domin neman abokan aiki. Duk da haka, mun san waɗannan tsare-tsare kuma muna aiki tare da sauran jami’an tsaro da gwamnatin jihar domin dƙiile yunƙurin ‘yan ta’adda.”

Wani tsohon Darakta a ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Mike Ejiofor, ya bayar da hujjar cewa, duk da cewa ƙungiyar ta kasance tun a shekarar 2018, hukumomin leƙen asirin ƙasar na sa ido kan ayyukansu. Ya ce, ’ya’yan ƙungiyar ba su da yawa da za su zama babbar barazana ga tsaron ƙasa.

Ya ce, “tabbas ta tabbata cewa, wannan ƙungiya ta kasance tun 2018. Ba sabuwar ƙungiya ba ce. Akwai ta tun 2018. Shugabannin al’umma ne suka shigo da su wajen yaƙar ’yan bindiga. ƙungiyar Nassala ce ta kafa wannan ƙungiya a Jamhuriyar Nijar. Don haka a lokacin da ya rasu, gwamnatin Nijar ta kasa shawo kansu.

“Don haka aka gayyace su don taimaka musu a Sakkwato. Akwai su, amma daga ƙarshe gwamnatin jihar Sakkwato ta sa su bar yankin ta hanyar tattaunawa. Wasu daga cikinsu sun kasance, kuma sun kasance suna aiki a sabuwar ƙungiya. Don haka ba wai sabuwar ƙungiyar ta’addanci ce ta ɓulla ba.

“Don haka suna wurin, kuma hukumomin leƙen asirin sun bi diddigin ayyukansu. Ba zan iya gaya muku ainihin adadin ba a yanzu, amma ba za su iya kawo babbar barazana ga tsaron ƙasarmu ba. Amma wannan ba yana nufin za mu bar su. Su ma ƙungiyar leƙen asirin suna bin ayyukansu.”

Ejiofor ya bayyana cewa, dole ne hukumomin tsaro su ƙara himma wajen leƙen asiri, sannan al’umma su tallafa wa waɗannan hukumomin, domin su taimaka wajen kawar da ƙungiyar ta’addanci.

Ya ce, “eh, watakila suna ƙoƙarin ɗaukar wasu mutane ne. Jami’an leƙen asirin na sa ido kan ayyukansu da nufin sanya su a tsari domin kada su samu gindin zama a yankin.

“Babu wani dalili na fargaba, amma ka da ku yi watsi da duk wata barazanar tsaro a ƙasar ba. Akwai abubuwa da yawa da za mu iya yi ta hanyar tallafin jama’a.”

Gaskiyar magana kan harin Mera da abinda ya biyo baya:

Bayan wata arangama da aka yi tsakanin al’ummar garin Mera da ke ƙaramar Hukumar Augie da kuma ’yan bindiga da ake sa ran ’yan ta’addar Lakurawa ne da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 17 ranar Juma’ar da ta gabata da kuma waɗansu Fulani bakwai da suka rasu ranar Asabar sanadiyyar kai musu harin ramuwar gayya da aka ce an yi, yanzu haka dai mahukumta suna nan suna neman warware bakin zaren, don ganin an sami zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin al’ummar garin Mera da Fulani mazauna yankin, kamar yadda aka saba.

Bayanan da Wakilin Blueprint Manhaja ya tattara daga mazauna garin na Mera, duk da ya ke dai ba su so a bayyana sunayensu ba, saboda hukumomi sun hana su maganganu, suna nuni da cewa bayan da waɗannan mutanen da a ke hasashen Lakurawa ne da suka zo ne ranar Juma’ar da ta gabata ne suka tara shanun mutanen garin sama da 100 ne ya harzuƙa mutanen, inda su kuma suka bi su a jejin suka yi bata-kashi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15, inda daga baya kuma aka sami ƙarin mutane biyu; adadin ya kai 17.

Wakilinmu ya kalato cewa, har wa yau bayan wannan harin na ranar Juma’a’a mutanen garin na Mera sun far wa mashekarin Fulani da ke zaune a wajen garin, inda suka hallaka Fulani bakwai, waɗansu da yawa kuma suka tsere da raunuka.

Kamar yadda wani mazauni garin na Mera ya bayyana, duk da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce, dalilin kai wa Fulani hari yana da nasaba da hasashen da ake yi na Fulanin suna da haɗin baki da waɗannan Lakurawa ne, saboda ba zai yiwu a ce dabbobin mutanen gari kawai a ke kamawa ba, ba a kama na Fulani, duk da ya ke suna zaune a jeji, haka-zalika kuma ana tuhumar waɗansu daga cikin Fulanin ne ke bai wa Lakurawa bayanan sirri game da mutanen garin.

A ɗaya ɓangaren kuma, Wakilin Blueprint Manhaja ya zanta da shugaban Fulani na ƙasar Augie, Alhaji Muhmmadu Rugga, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ƙara da cewa, yanzu haka mutanensu duk sun tarwatse, ba a san inda waɗansu suke ba sanadiyyar harin ramuwar gayya da mutanen garin Mera suka kai musu ranar Asabar da yamma, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Fulani bakwai.

Ya ce, ba ɓarayin dabbobi ko waɗansu baƙi ne daga wani waje ba ne suka kai musu hari ba, mutanen garin Mera ne, kamar yadda mahaifiyar yaran da aka kashe ta bayyana.

Ya ce, yanzu dai su ba wani abu su ke nema ba illa dai hukuma ta shigo a zauna a nemo hanyar da za a zauna lafiya tsakaninsu da sauran al’umma, saboda ba su da wani waje da ya fi nan, domin a nan aka haifi iyayen iyayensu har zuwa kansu.

Malam Muhammadu ɗanbaba, wani Bafillace mazaunin garin na Mera, ya zanta da Wakilin Blueprint Manhaja kuma ya bayyana cewa, shi yaransa huɗu da suka haɗa da Basiru da ɗan Ali da Aliyu da kuma Nana Asma’u aka kashe ranar Asabar da yamma lokacin da mutanen garin Mera suka kai musu hari a gidansa da ke daga wajen garin ta hanyar sara da adda, kuma bayan kashe waɗannan yaran nasa aka banka wa gidansa wuta, wanda ya yi sanadiyyar tarwatsewar al’ummar Fulanin, saboda tsananin tashin hankali.

Alhaji Bashir Isah Mera (Yeriman Mera), wani jigo a garin na Mera, ya bayyana cewa, shi dai abinda ya tabbatar shine an kashe waɗansu Fulani biyu, waɗanda suna daga cikin masu tsegunta wa ’yan bindigar bayanai (informer) ne, kuma an gan su da bindiga. Saboda haka mutane ba su yi wata-wata ba, da aka kama su, nan take suka far musu suka kashe su kuma jami’an ’yan sanda sun ɗauki gawarwakinsu haɗi da bindigogi da aka gani a hannunsu da wayoyin salula.

Ya kuma yaba wa Gwamantin Jihar Kebbi bisa ɗaukar matakin gaggawa da ta yi lokacin da wannan abin ya faru.

Alhaji Abubakar Sadik Augie, mai baiwa gwamna shawara kan tallafin Gwamnatin Tarayya, ya bayyana wa wakilinmu cewa, yanzu haka Gwamantin Kebbi tana nan tana duba hanyoyin da suka kamata, don tabbatar da tsaro a wannan yankin, saboda kauce wa afkuwar irin wannan nan gaba.

“Ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin mun samar da sahihan bayanai, don ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakin da ya dace kuma muna nan muna aiki tare da mutanen garin da kuma ɓangaren gwamnati da kuma Fulani da mu ke zaune tare da su shekaru aru-aru, don ganin an sami zaman lafiya mai ɗorewa tsakanin al’ummar garin Mera da Fulani,” inji shi.

Shugabaan ƙaramar Hukumar Augie, Hon. Yahaya Muhammed Augie, ya zanta da Wakilin Blueprint Manhaja a garin na Mera da ake zaman makoki, inda ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya nuna alhininsa bisa ga afkuwar wannan lamarin.

Ya ce, “ba shakka dangantakar mutanen wannan yankin da Fulani daddiyar dangantaka ce ta kakanni da iyaye kuma insha Allahu bakin wuta ba zai mutu a hannunmu ba, mu ma za mu riƙe su a matsayin ’yan uwa, ba abokan gaba ba.

“A matsayinmu na Musulmi, ya zama wajibi mu ɗauki abin a matsayin muƙaddari daga Allah, saboda babu wata makawa, tabbas sai ya faru.”

Ya yi godiya ga gwamnatin ta Kebbi bisa ga saurin kawo agajin jami’an tsaro da kuma gudunmawar Naira milliyan 50, don raba wa iyalan mamata da waɗanda suka sami raunuka zuwa waɗanda aka sacewa dabbobi. 

Haka zalika ya ja kunnen al’ummar yankin da su duƙufa wajen addu’ar Allah ya tona asirin duk wani mutum ko wata ƙungiyar da ke tsegunta wa ’yan bindigar bayanai (informer), saboda ba wani mahaluki da ya san su sai dai a dage da addu’ar Allah ya tona asirinsu.

Ya kuma yi ƙarin haske dangane da halin da a ke ciki, inda ya ce, yanzu haka dai Gwamnatin Jihar Kebbi ta haɗa wani kwamitin sulhu da kuma maido da zama lafiya na musamman tsakanin al’ummar garin Mera da Fulani da ke zaune tare.

Haka zalika kuma a baya-bayan nan ya yi ƙarin haske dangane da irin cigaban da ake samu, inda ya ce, an sami nasarar gano shanu da ’yan bindigar suka ƙwace a sansaninsu da ke jejin wani ƙauye da a ke kira Kalgo a kan iyakar jihohin Kebbi da Sokoto da ke ƙaramar Hukumar Binji.

Sai dai kuma ya bayyana cewa, babu waɗansu jami’an soja da suka yi faɗa da ’yan bindigar illa dai ana hasashen ’yan bindigar sun tsorata ne sun gudu sun bar wajen, saboda ganin irin shirin da aka yi na fuskantar su.

ɗaya daga cikin ’yan sa-kai daga garin na Mera ya shaidawa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, Lakurawan sun gudu sun bar ladarsu kuma ba gudu ba ja da baya kuma a kowane lokaci a shirye su ke da su fuskanci yan bindigar.

“Mun tafi sansanoni uku na ’yan bindigar. amma babu kowa, duk sun gudu, amma dai mun sami ganin shanu 41 a ranar Talata kuma yau Laraba mun gano 17 mun kuma koro su zuwa garin Mera, don hannanta su ga masu su,” inji shi.

A daren Larabar da ta gabata wani Bafillace da bai so a bayyana sunansa ba mazauni ƙauyen Kamfani a ƙaramar Hukumar Argungu, ya labarta wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, suna kan hanyar dawowa daga kasuwar Amagwaro a ƙaramar Hukumar Arewa sun ga Lakurawan suna tsallaka titi a wata hanya kusa da garin Bui kan babura a cikin dare.

An tattaro wasu bayanan ne daga jaridar Premium Times

By ukarofi