Daga USMAN KAROFI
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Daniel Bwala a matsayin mai ba shi Shawara na musamman kan harkokin watsa labarai da sadarwa na fadar gwamnati kamar yadda sanarwar da Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman ya fitar a ranar Alhamis ta bayyana.
Bwala, wanda ya taba zama hadimi ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya goyi bayan Atikun a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda Atiku ya faɗi a hannun Tinubu. Bayan zaɓen, Bwala ya canza sheka zuwa ga goyon bayan Tinubu matakin da ya jawo cece-kuce dayawa.
Onanuga ya kuma tabbatar da naɗa wasu mutum uku a matsayin shugabannin hukumomi daban-daban na gwamnati:
Mr. Olawale Olopade ya zama Darakta Janar na hukumar wasanni ta ƙasa. Olopade, wanda ya ƙware a harkokin wasanni, ya taɓa zama kwamishinan matasa da wasanni a Jihar Ogun kuma ya jagoranci kwamitin shirya gasar wasannin Ƙasa na 2024.
Dr. Abisoye Fagade an naɗa shi a matsayin Darakta Janar na hukumar kula da harkokin yawon buɗe ido ta Ƙasa. Fagade masani ne a harkokin kasuwanci da sadarwa, kuma shi ne wanda ya kafa kamfanin Sodium Brand Solutions.
Dr. Adebowale Adedokun ya zama Darakta Janar na hukumar kula da siyar da kayayyakin gwamnati. Kafin wannan muƙamin, Adedokun shi ne daraktan bincike, horaswa da tsare-tsare na wannan hukumar.
Waɗannan naɗe-naɗen suna nuna cigaba da ƙoƙarin shugaba Tinubu na bunƙasa ƙwarewa da jagoranci a manyan hukumomin gwamnati.
