Sojojin sama sun hallaka ƴan bindiga 15 a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta yi nasarar hallaka ƴan bindiga 15 a wani hari ta sama da ta kai wa dabar ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Safana dake Jihar Katsina.

Zagazola Makama, wanda masani ne kan aikace-aikacen ƴan ta’adda, ya ce sojojin sun ƙaddamar da harin ne a wata maɓoyar ƴan bindinga dake ƙauyen Tsaskiya.

Makama ya kuma ce rundunar sojin ‘Fansar Yamma’ ce ta yi luguden wutar da nufin tarwatsa wasu manyan sansanonin ɓarayin daji dake yankin.

Wasu bayanan sirrri daga majiyar sojin, ta bayyana cewa, “rundunar sojin sama ta samu nasarar hallaka ƴan ta’adda bayan wani luguden wuta ta sama. aƙalla ƴan bindinga 15 sun rasa rayukansu a yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindinga.”

Kazalika, majiyar ta ce aƙalla mutane biyar da ɓarayin suka yi garkuwa da su sun samu kuɓuta daga inda ake tsare da su sakamakon tarwatsa sansanin ƴan bindingar.

By Babaji