
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Makarantun kiwon lafiya 14 masu zaman kansu Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rufe su bisa rashin cika ƙa’idoji yayin da wasu 7 kuma aka umarci da su yi wasu gyare-gyare.
An kuma bai wa wasu makarantu 8 izinin cigaba da aikin su.
Mai bai wa gwamna shawara kan makarantun kiwon lafiya Hon. Umar Mamuda ya sanar da hakan a hira da manema labarai a ofishinsa.
Ya ce wannan mataki da gwamnati ɗauka ya biyo bayan sakamakon da kwamitin binciken da gwamnatin ta kafa ya fitar ga harkokin gudanarwar waɗannan makarantu masu zaman kansu.
Kwamitin da ya ƙunshi daraktoci na Ma’aikatar kiwon Lafiya ta jihar da wasu likitoci masu zaman kansu waɗanda suka ɗauki mako uku su na tantance makarantun.
Hon. Mamuda ya bayyana cewa su waɗannan makarantu 14 da aka rufe an same su ne da laifin rashin samun takardar izinin gina wajen karatu, ingancin malamai da tsarin koyarwa.
Ya kuma ce gwamnati na duba yiwuwar tallafa wa ɗaliban da abin ya shafa domin su cigaba da karatunsu.
Jama’a dai sun yi ta ƙorafi game da buɗe ire-iren waɗannan makarantu barkatai wanda hakan ya sanya alamar tambaya game da ingancinsu.
Hakan yasa Gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa kwamitin tantance makarantun da nufin gano na bogi.
