Jami’an CWC sun kama jami’in kiwon lafiya mai yi wa ƴan ta’adda magani a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jami’an tsaron al’umma na community watch corps (CWC), sun kama wani malamin asibiti mai sun Rabe Mamman da laifin kula da lafiyar ƴan ta’adda a ƙaramar hukumar Batsari dake Jihar Katsina.

A yayin wata hira da jami’an CWC da manema labarai, jami’in ya tabbatar da zargin da ake masa.

Ya ce akwai lokacin da ya taɓa yi wa wani ƙasurgumin ɗan ta’adda mai suna Abu Raɗɗe magani a rauni da ya samu sakamakon artabu da ya yi da mutanen ƙauyen Kirtawa.

“An taɓa kira na ƙauyen Baranda inda na yi wa shi babban ɗan bindiga, Abu Raɗɗe magani a rauni da ya samu bayan ƙazamin faɗa da mutanen ƙauyen Kirtawa”, inji malamin asibitin.

Ya kuma ce shi ɗan asalin garin Dodo ne a ƙaramar hukumar Batsari, kuma yana da shagon sayar da magani a ƙauyen.

Ya ƙara da cewa, wannan ba shine karo na farko da ya ke yi wa ƴan ta’adda magani ba idan rashin lafiya ya kama su ko sun samu rauni.

By Babaji