Jakadan Falasɗinawa ya buƙaci duniya ta tabbatar da kare haƙƙin bil’adama a Gaza

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Jakadan Falasɗinawa a Nijeriya, Abdullah M. Abu Shawesh, ya bayyana damuwarsa kan cigaba da kashe-kashen da ake yi a Gaza tare da kiran a kawo ƙarshen hare-haren Isra’ila. Yana mai cewa lokaci ya yi da ƙasashen duniya za su ɗauki matakin kawo ƙarshen “yunƙurin kisan ƙare dangi da kuma tsangwamar da aka daɗe ana yi wa al’ummar Falasɗinu.

Bisa ƙididdigar da aka fitar a kan rikicin Gaza, fiye da kwanaki 405 na takurawa da kashe-kashen da Isra’ila ke yi tare da goyon bayan Amurka, mutane 43,603 na Falasɗinawa ne aka kashe, yayin da aka jikkata mutane 102,929 a Gaza, galibi yara da mata. Ya ƙara da cewa, “Wannan adadi yana iya kasancewa kaɗan ne saboda akwai mutanen da suka mutu ko suka jikkata amma har yanzu suna ƙarƙashin rusassun gine-gine.”

A ɓangaren yammacin gaɓar kogin Jordan, an kashe mutane 811 daga cikin Falasɗinawa, an raunana mutane 5,755, sannan aka kafa shingen soji kusan 13,585. Bugu da ƙari, a yankunan yammacin gaɓar Kogin Jordan, adadin waɗanda aka tsare ya kai 11,600 wanda ya haɗa da mata 430 da yara 760 da kuma ‘yan jarida 132 ciki har da 85 da ke hannun hukumomin Isra’ila. Haka kuma akwai rahotannin cin zarafi, duka da rushewa ko kwace kadarorin Falasɗinawa da suka haɗa da dukiya da zinare.

Shawesh ya bayyana cewa, a yanzu haka Isra’ila tana amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi a Gaza, musamman a Arewacin Gaza, inda ake barin motocin kaya 30 kawai su shiga kullum wanda ke da kashi 6% na buƙatun yau da kullum. Wannan takura wa al’umma ya sanya rashin abinci ya yi tsanani, wanda ke da tasirin lafiyar ɗan Adam a yanzu da kuma nan gaba.

A cewarsa, Falasɗinawa da ke Arewacin Gaza na fama da ƙunci yayin da suke ci gaba da fuskantar hare-hare, tare da rashin abinci, ruwa, da magunguna. “Duk wanda ya yi ƙoƙarin barin yankin don neman waɗannan kayayyakin yana fuskantar haɗarin kashewa daga jiragen yaƙi na Isra’ila,” in ji Shawesh. Ya yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta ɗauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron rayuka da kuma kare haƙƙin bil’adama.

Jakadan ya bayyana cewa a cikin watannin da ke tafe, Isra’ila na shirin faɗaɗa mulkin ta zuwa yammacin gaɓar Kogin Jordan tare da nufin mallake yankin baki ɗaya. Ya bayyana cewa wannan yunƙuri zai kasance ƙarshe ga shirin samar da zaman lafiya da kuma mafita ta ƙasashe biyu ga rikicin Isra’ila da Falasɗinu.

By ukarofi