Daga USMAN KAROFI
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga mutanen Jihar Ondo da su sake zaɓen Gwamna Lucky Aiyedatiwa tare da mataimakinsa, Dr. Olayide Adelami a zaɓen gwamna da za a yi ranar Asabar mai zuwa. Shettima ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa, idan aka sake zaɓen Aiyedatiwa jihar za ta ƙara samun ci gaba, zaman lafiya da wadata.
Sanata Shettima ya yi wannan kiran ne a wajen taron kammala yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da aka yi a filin dimokraɗiyya na MKO Abiola a Akure inda ya ce zaɓen gwamna Aiyedatiwa ba kawai na neman muƙami ba ne, amma don kawo ci gaba da haɗin kai ga dukkan yankuna na jihar Ondo. Ya buƙaci masu jefa kuri’a su tabbatar da cewa, ƙuri’unsu saƙo ne ga waɗanda ke tantamar ƙarfin al’ummar jihar.
Haka zalika, Shettima ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana tare da Gwamna Aiyedatiwa cikin cikakken goyon baya duk da kasancewarsa a taron bunƙasa ƙasashen Afirka a Saudi Arabiya. Ya ce Shugaban Ƙasa ya amince da nasarar Aiyedatiwa a matsayin wanda zai ci gaba da kula da walwalar al’ummar Ondo.
A lokacin da yake jawabi, Gwamna Aiyedatiwa ya buƙaci jama’a su fito su jefa ƙuri’u ga APC, yana mai bayyana cewa marigayi tsohon gwamna Rotimi Akeredolu ya taɓa bayyana masa cewa zai gaje shi. Ya kuma yi shiru na tsawon daƙiƙa domin tunawa da marigayi Akeredolu, inda ya tabbatar wa al’ummar jihar da ci gaba idan aka sake zaɓensa.
Taron yaƙin neman zaɓen ya samu halartar manyan jiga-jigan APC, ciki har da shugaban gwamnonin Nijeriya AbdulRahman AbdulRazaq, gwamnan Jihar Kwara, Hope Uzodimma na Jihar Imo da sauran gwamnonin Ogun, Legas, da Ekiti tare da shugaban yaƙin neman zaɓen Ondo na APC, Sanata Ovie Omo-Agege da tsohon mataimakin gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu.
