Arewa za ta sake shiga duhu bayan ‘yan bindiga sun sake lalata tashar wuta a Kogi

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya yi gargaɗin cewa ana iya fuskantar matsalar rashin wuta a ƙasar nan, bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari tashar rarraba wuta a Obajana, Jihar Kogi. Babban manajan hulɗa da jama’a na TCN Ndidi Mbah, ta bayyana hakan a wata sanarwa da hukumar ta fitar , inda ta ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da yammacin ranar Talata.

A cewar Mbah, rahotannin daga jami’an tsaro da ke wurin sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun fara harbi ba tare da ƙaƙƙautawa ba, lamarin da ya sa jami’an tsaron wurin tserewa don tsira da rayukansu. A yayin harin, sun harbi wata babbar na’urar wutar lantarki mai ƙarfin 150MVA da aka sanya a wurin, wanda hakan ya haifar da lalacewar na’urar. TCN ta ce tana aiki tare da kamfanin da ke kula da aikin domin tantance irin ɓarnar da aka yi da kuma yadda za a magance ta.

Kamfanin TCN ya ce wannan hari wani ɓangare ne na ƙaruwar hare-haren lalata kayan aikin rarraba wutar lantarki a faɗin ƙasar. Sabuwar tashar rarraba wutar lantarkin Obajana da ake ginawa na da ƙarfin 1X150MVA 330/132/33kV, wadda aka yi nufin za ta taimaka sosai wajen inganta wutar lantarki a jihar Kogi da yankunan da ke kusa idan aka kammala aikin.

Ana ci gaba da samun ƙaruwar lalata kayan aikin wutar lantarki a Nijeriya, wanda ke janyo cikas a fannin samar da wuta ga al’umma. A shekarar 2024 kaɗai, an sami rahoton lalata aƙalla ginshiƙan wutar lantarki guda 20 a faɗin ƙasar ciki har da harin da aka kai wa layin wuta mai karfin 330kV daga Lokoja zuwa Gwagwalada a makon jiya.

Kamfanin TCN ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki tsauraran matakai wajen kare kayan aikin wuta domin magance irin wannan matsala da ke janyo hasara mai yawa ga ƙasar da kuma kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya

By ukarofi