Fashewar Gas ya yi sanadiyar jikkata mutane da dama da lalata dukiyoyi a Katsina

Spread the love

Wata mota ɗauke da gas ta fashe a unguwar Magama, ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina a ranar Juma’a, inda mutane da dama suka samu raunuka, haka kuma aka samu lalacewar motoci da gidaje kamar yadda News Point Nigeria ta tabbatar.

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wata tashar mai mai suna ‘Walidan’, inda ake zargin an ɓoye wasu kayayyakin da ake zaton an shigo da su cikin ƙasa daga Jamhuriyar Nijar.

Wani mazaunin Magama, Aliyu Muhammad, ya ce, “Lamarin ya faru ne lokacin da aka ajiye wata mota ɗauke da gas a tashar mai tsawon kwanaki. Motoci bakwai sun kone, gidaje biyu sun lalace, ciki har da ginin da ya ɗauki tashar mai da wani gidan kusa.” Aliyu ya ƙara da cewa mutane da dama sun samu raunuka a wajen.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yan Sanda na Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce, “A yau, 15 ga Nuwamba, 2024, da misalin karfe 8:45 na safe, jami’an ‘yan sanda a Jibia sun ji ƙaran fashewa mai karfi. Da gaggawa DPO ya jagoranci jami’an tare da sojoji zuwa wajen da lamarin ya faru.”

ASP Aliyu ya bayyana cewa, an samu ƙonewar motoci guda shida, amma babu asarar rai, yayin da tawagar tsaro ta ɗauki matakan kare rayuka da kuma rage lalacewar dukiya, tare da kashe wutar.

Kwamishinan ‘yan Sandan Jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya umurci a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin fashewar. Za a ci gaba da sanar da jama’a yadda binciken zai ci gaba da tafiya.

By ukarofi