An zargi hukumomin tsaron Nijeriya da gaza kare layukan lantarki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumomin tsaro a Nijeriya na cigaba da fuskantar suka kan gazawarsu wajen kare layukan lantarkin ƙasa daga ɓarayi, lamarin da ke janyo katsewar wutar lantarki da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki.

Duk da hukumomi da yawa da abin ya shafa, manyan layukan lanataki sun yi rauni saboda rashin isasshen kariya.

Yawaitar hukumomin leƙen asiri da tsaro a ƙasar wani lamari ne mai matuƙar muhimmanci, amma duk da haka ba a samun abin da ya dace.

Yayin da ake da hukumomi da yawa da abin ya shada, akwai ƙalubale wajen tantance wanda ke da alhakin kare layukan lantarki.

Rashin isassun kuɗaɗe, rashin tsare-tsare na dogon lokaci, da kuma rashin gudanar da aiki sune manyan ƙalubalen da hukumomin tsaro ke fuskanta.

Waɗannan gazawar sunahaifar da sakamako mai tsanani, waɗanda suka haɗa da katsewar wutar lantarki, asarar tattalin arziki, da kasadar tsaron ƙasa.

Masana sun buƙaci gwamnati da ta yi garambawul ga hukumomin tsaro da ababen more rayuwa domin tunkarar waɗannan ƙalubale.

Shawarwari sun haɗa da daidaita ayyukan hukuma, ƙara tsaro, da aiwatar da tsare-tsare na dogon lokaci don tabbatar da tsaron ƙasa.

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin sake duba tsarin tsaron ƙasa don magance matsalar rashin aikin yi.

Cigaban tattalin arzikin Nijeriya da tsaron ƙasa ya dogara ne da ingantaccen tsarin ƙasa. Dole ne gwamnati ta ba da fifiko ga wannan muhimman ababen more rayuwa don hana ci gaba da kawo cikas da tabbatar da ci gaban ƙasar

By ukarofi