LAFIYA UWAR JIKI: Illoli 10 na yawan shan maganin gajiya

Spread the love

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Akwai rukunin maguguna masu ɗauke ciwo musamman na gaɓɓai, gajiya da kumburi da ake kira da NSAIDs. Misalansu sun haɗa da ‘ibuprofen’, ‘ibumol’ da ‘diclofenac’. 

Idan mutum ya ɗabi’antu da shan waɗannan maguguna to ya na jefa kansa ko kanta cikin haɗarin samun waɗannan matsaloli: 

1. Ciwon olsa:

Wanda na yi bayaninta sosai a baya. Da ka ji gajiya ko ciwo ka jawo ‘diclo’ ka sha. Hakan bashi da kyau. Zai iya jawo maka olsa domin kuwa yana ɗaɗe shimfidar da ke tumbinka, wasu lokuta ma har ya huda ta, sai a samu zubar jini daga ciki, sai mutum ya dinga bayan gari mai duhu ko baƙi.

2. Lalacewar ƙoda:

Akwai nau’i 2 na lalacewar ƙoda. Na farkon shine wanda bai fi wata 3 ba (Acute Kidney Injury), sai kuma wanda ya haura wata 3 yana lalacewa (Chronic Kidney Disease). Wannan shi mu ke cewa ciwon ƙoda. To, yawan shan waɗannan magunguna kan iya jawo kowanne, ko na farkon ko na biyun. 

3. Matsalolin zuciya:

Ya kan iya jawo matsaloli irinsu Hauhawar jini, da Bugawar Zuciya. 

4. Matsalolin hanta:

Irinsu ciwon hanta (Hepatitis) ko gazawar hanta, wato ‘Liɓer Failure’. 

Sauran matsalolin su ne;

5. ƙwannafi.

6. ƙarancin jini.

7. Kumburin Jiki.

8. Hujewar hanji.

9. Allaji, kamar su ƙuraje, borin jini da irinsu.

10. Tashin cutar asma ga waɗanda su ke da ita.

Naku MI ABDULLAHI

By ukarofi