Amarya ta mutu tana tsaka da rawa a wajen bikinta

Spread the love

Ranar biki ta koma ranar baƙin ciki ga ɗaukacin dangin ango da amarya lokacin da wata amarya da aka bayyana sunanta da Sorelle ta yanke jiki ta faɗi ta mutu yayin da take rawa a wajen liyafar ranar aurenta.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Tuwita, tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya rubuta cewa, “Abin baƙin ciki ne da jin cewa amarya Sorelle ta faɗi kuma ta mutu yayin da take rawa a ranar aurenta.

Yana da muhimmanci mutane su fahimci cewa a cikin ‘yan kwanakin nan ana yawan samun mutuwar fuju’a, inda mutane kan mutu babu ciwo, babu haɗari. “

Har zuwa lokacin haɗa waɗannan rahoton, har yanzu ba a san dalilin da ya haddasa mutuwar amaryar ba.

By ukarofi