Neja na sa ran girbin tan miliyan ɗaya na masara – Gwamna Bago

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja ya kiyasta girbin sama da tan miliyan ɗaya na masara daga gonakin jihar a wannan kakar, inda ya yi alƙawarin yin fallasa masu tara kayan abinci a jihar domin daƙile tashin farashin kayayyaki.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ƙarshen makon da ya gabata a lokacin da yake ƙaddamar da noman masara a ɗaya daga cikin gonakin Neja, ta hanyar amfani da sabon fasahar girbi.

Ya ce, “Yin amfani da fasahar girbin, zai rage asara tsakanin kashi 80 zuwa 90 cikin ɗari. Muna sa ran kusan tan miliyan ɗaya na masara a bana ban da shinkafa, waken soya da gero.”

Ya kuma gargaɗi waɗanda ke da hannu wajen tara kayan abinci da su gaggauta daina aikata hakan daga jihar Neja domin gujewa fushin dokar, inda ya ƙara da cewa: “Na umurci hukumar kula da farashin kayayyaki ta jiha da ta gaggauta samar da matakan da za su daƙile ayyukan hada-hadar kuɗi tare da gano kayan abinci da ke cikin rumbunan wasu, wanda yakan haifar da hauhawar farashin kayayyakin abinci.”

Ya ce, gwamnatin ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta cimma manufofinta na ciyar da al’ummar ƙasa ta hanyar noma.

A halin da ake ciki, gwamnan ya ziyarci al’ummar Emi Guye da ke kewayen gonar, inda ya ba da umarnin a samar da wasu ababen more rayuwa kamar ruwa da hasken rana ga al’ummar.

Hakimin ƙauyen Emi Guye, Alhaji Usman Mohammed, wanda ya yi magana a madadin jama’a, ya yaba wa gwamnan tare da yaba masa bisa ci gaban da yake samu a jihar.

By ukarofi