Yadda gwamnoni suka ciyo bashin Tiriliyan N11.4

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Bashin da ake bin jihohin Nijeriya ya ƙaru zuwa Naira Tiriliyan 11.47 a ranar 30 ga watan Yunin 2024 duk da ƙarin kaso da suka samu daga kwamitin rabon asusun tarayya, FAAC.

An bayyana hakan ne a cikin wani bincike daga rahoton bashin jama’a da Ofishin Kula da Bashi ya fitar.

A farkon shekarar 2024, an samu ƙaruwar kashi 14.57 cikin ɗari daga tiriliyan N10.01 da aka ciyo a watan Disamba 2023.

ƙarin ya samo asali ne sakamakon hauhawar cin basuka daga waje, wanda ya ƙara taɓarɓara sakamakon faɗuwar darajar Naira.

Bashin waje na jihohi da babban birnin tarayya ya haura daga Dala Biliyan 4.61 zuwa Dala Biliyan 4.89, wanda hakan ya nuna ƙaruwar kashi 6.14 cikin 100.

Sai dai kuma a fannin Naira, wannan adadi ya haura da kashi 73.46 bisa ɗari, daga tiriliyan N4.15 zuwa tiriliyan N7.2, biyo bayan faɗuwar darajar Naira daga N899.39 a dala 1 a watan Disamba 2023 zuwa N1,470.19 a dala 1 zuwa watan Yunin 2024.

Basusukan cikin gida na jihohi da babban birnin tarayya Abuja, ya samu koma baya sosai da kashi 27.12 cikin ɗari, inda ya ragu daga tiriliyan N5.86 zuwa tiriliyan N4.27.

A jimilce jihohi da babban birnin tarayya Abuja sun kai kashi 8.54 bisa 100 na bashin Nijeriya na tiriliyan N134.3 a watan Yunin 2024, ya sauka daga kaso 10.29 cikin 100 a watan Disambar 2023, duk da cewa yawan basukan da suka karɓa ya ƙaru.

By ukarofi