Gwamnatin Fubara ta kere ta Wike wajen sama wa Ribas kuɗin shiga

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Siminalayi Fubara a Jihar Ribas ta samu Naira Biliyan 726 a matsayin kuɗaɗen shiga a cikin kaso uku na shekarar 2024, kamar yadda rahoton kasafin kuɗi na jihar Ribas (BPR) ya nuna.

Wannan adadi dai jimillar duk kuɗaɗen shiga ne da gwamnatin jihar ta samu, waɗanda suka haɗa da na kaso daga asusun tarayya (FAAC), kuɗaɗen shiga na cikin gida da ake kira ‘Internal Generated Reɓenue’ (IGR) da dai sauran su, duk a shekarar 2024.

Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da Tsare Tattalin Arziki ne ke samar da rahoton BPR a duk wata, tare da haɗin gwiwar ofishin Akanta Janar da Ma’aikatar Kuɗi, wanda ana bugawa a shafin yanar gizon gwamnati.

Takardar ta nuna cewa daga watan Janairu zuwa Satumba, hukumar FAAC da IGR sun zarce kasafin kuɗin shekarar 2024, wanda hakan ya nuna cewa jihar ta samu ɗimbim kuɗaɗen shiga duk kuwa da rikicin siyasa na tsawon shekara ɗaya.

Wani abin lura shi ne, duk da tashe-tashen hankulan siyasa da hauhawar farashin kayayyaki, tattalin arzikin jihar ya kai wani matsayi mai girma, inda ta samar da sama da Naira biliyan 30 a rubu’i na uku na shekarar 2024.

By ukarofi