Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Alamu masu ƙarfi sun nuna cewa Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ka iya gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga taron haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta ƙasa a cikin makon farko na Disambar wannan shekara, amma har yanzu babu wani tsarin da ya tabbatar da hakan.
Majalisar Dattawa ta hannun kwamitinta kan harkokin kuɗi, ta bayyana cewa yanke shawarar gabatar da kasafin kuɗin 2025 ya ta’allaƙa ne ga ɓangaren zartarwa na gwamnati ƙarƙashin jagorancin shugaba Tinubu.
Idan dai ba a manta ba, kamar yadda aka saba tun lokacin zaman majalisar wakilai ta 9 tare da haɗin gwiwar shugaban ƙasa na wancan lokacin, Muhammadu Buhari, ana gabatar da ƙididdigar kasafin kuɗi na shekara ne a cikin makon farko na watan Oktoba, inda aka buƙaci a riƙa amfani da wasu tsarin wajen aiwatar da hakan kamar tsarin kuɗi na MTEF da takarda dabarun kuɗi na FSP, waɗanda dole sai an gabatar da su don samun cikakken kasafin kuɗi.
MTEF da FSP a ƙarƙashin Buhari, ana karɓar su ne a cikin watan Satumba don gudanar da ayyukan da suka dace da hukumomin samar da kuɗaɗen shiga ta kwamitocin kuɗi a majalisun biyu na ƙasa.
Dangane da jinkirin da aka samu wajen gabatar da kasafin har zuwa watan Nuwamba, ‘yan jarida a ranar Juma’ar makon da ya gabata sun tambayi shugaban kwamitin kuɗi na majalisar dattawa, Sanata Mohammed Sani Musa (APC Neja ta Gabas), kan lokacin da kasafin kuɗin shekarar 2025 zai iso gaban majalisa.
Sanata Musa da ya ke amsa tambayar ya ce, yanke shawara kan hakan ya rataya ne ga ɓangaren zartarwa ba majalisar dattawa.
“Ya kamata shugabannin zartarwa su sami damar amsa wannan tambayar, saboda na san suna yin aikinsu yadda ya kamata.
“A matsayina na shugaban kwamitin majalisar dattijai kan kuɗi tare da mambobin kwamitin, sun tattauna da ministan kuɗi, babban jami’in kamfanin man fetur na Nijeriya (NPL) da sauran manya a bangaren tattalin arzikin ƙasar nan kan yadda kasafin kuɗin shekarar 2024 zai kasance.
“Tabbas suna aiki akan kasafin kuɗin 2025 kuma za su tura mana shi idan aka kammala. Hukuncin hakan yana kan ɓangaren zartarwa ne ba mu a Majalisar Dokoki ta ƙasa ba,” inji shi.
Idan dai za a iya tunawa, Shugaba Tinubu ya gabatar da ƙididdigar kasafin kuɗin shekarar 2024 ga zaman haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta ƙasa a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023 wanda aka jinkirin amincewa da shi daga Majalisar Dattawa da ta Wakilai zuwa ranar Asabar 30 ga Disamba, 2023 tare da sanya hannu kan dokar a watan Janairun 2024.
Ko da a matakin zartarwa, har yanzu ba a ambata ba, na Tsarin Kuɗi na Matsakaici na 2025 – 2027 (MTEF) wanda zai ƙunshi sigogi waɗanda ƙididdigar kasafin kuɗi na 2025 za su kasance kamar ma’auni na farashin mai, hasashen samar da mai a kowace rana, musayar farashin Naira zuwa dalar Amurka, hauhawar farashin kayayyaki da dai sauransu.
Sai dai shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kuɗi da ministan kuɗi da kuma ministan tattalin arziki, Wale Edun, sun tabbatar wa ‘yan Nijeriya bayan zaman tattaunawa da suka yi a ranar Juma’a, hasashe ya fara bayyana a ƙarshen ramin sake fasalin tattalin arzikin gwamnati.
Sanata Musa ya ce, “Na yi imani da tabbacin da Ministan Kuɗi ya bayar na cewa tattalin arzikinmu yana samun kyakykyawan tsari ta hanyar samun sakamako daga gyare-gyare.
“Misali, adadin bashinmu zuwa GDP yana saukowa sosai zuwa kusan 60. Alamu masu kyau suna ci gaba da nunawa kuma nan da watanni 16 zuwa 18 masu zuwa, ‘yan Nijeriya da kansu za su ga nasarorin a aikace.”
