Farashin kayan gini ya yi tashin gwauron zabi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hauhawar kayayyakin gine-gine a Nijeriya a halin yanzu yana shafar kadarori, lamarin da ke zama babban ƙalubale ga yunƙurin gwamnati na samar da gidaje masu saukin kuɗi.

Haka kuma lamarin ya shafi masu sana’ar kadarori masu zaman kansu, domin da yawa daga cikinsu sun ja baya a kan gine-gine, yayin da ɗaiɗaikun mutane masu sha’awar gina gidajensu su ma ke ƙorafi.

Har ila yau, masu sayar da kayayyakin gini sun ce kasuwar ta tsaya cak saboda mutane ba sa iya sayen kayan.

Binciken kasuwa da kafafen yaɗa labarai suka yi ya nuna cewa farashin kayayyakin gini ya ƙaru kusan kashi 100 cikin 100.

Lamarin dai ya haifar da cikas a harkar gine-gine, inda ya haifar da ƙalubale ga manya-manya da ƙananan masu masu gidaje.

Ana danganta hakan ne da wasu abubuwa da suka haɗa da taɓarcarewar hanyoyin samar da kayayyaki, hauhawar farashin aiki da kuma hauhawar farashin kaya ta hannun dillalai idan aka kwatanta da farashin masana’antu.

Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa, hauhawar farashin kaya a Nijeriya a watan Satumban 2024 ya ƙaru zuwa kashi 32.70 cikin ɗari, daga kashi 32.15 cikin 100 a watan Agustan 2024, wanda ya nuna ƙaruwar kashi 0.55 a duk wata.

Hukumar NBS ta ƙara da cewa hauhawar farashin kayayyaki a cikin watan ya biyo bayan ƙarin farashin sufuri da kuma farashin kayan abinci.

Hakanan, hauhawar farashin kayayyaki a birane a watan Satumba na 2024 ya kasance kashi 2.67 cikin ɗari, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 0.28 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 2.39 cikin ɗari a watan Agustan 2024; yayin da hauhawar farashin kayayyaki a yankunan karkara ya tsaya da kashi 2.39 a watan Satumbar 2024, wanda ya ƙaru da kashi 0.33 cikin dari daga kashi 2.06 cikin 100 da aka samu a watan Agustan 2024.

Sakamakon wannan matsin lamba na hauhawar farashin kayayyaki, an sami raguwar ayyukan gine-gine yayin jama’a ke kokawa da tsadar.

Wani bayani daga bankin Shelta Afriƙue ya nuna cewa giɓin gidaje a Nijeriya ya kai kimanin miliyan 27, wanda shi ne kusan kashi 40 cikin 100 na giɓin da nahiyar ke fuskanta.

By ukarofi