Hizbullah ta tabbatar da mutuwar kakakinta a harin Beirut

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar Hizbullahi ta tabbatar da mutuwar mai magana da yawunta, Muhammad Afif a wani hari da Isra’ira ta kai a Beirut.

Afif wani jigo ne a harkokin jaridar Hizbullahi, wadda ƙungiya ce ta ƙasar Iran, kamar yadda ta wallafa a kafar Telegram.

Baya ga kashe jagoran ƙungiyar, Afif shi ne sanannen mutum na biyu da aka kashe wanda kwanan nan ya jagoranci wani taron manema labarai.

Haka nan Afif ya kasance na hannun daman tsohon babban sakataren ƙungiyar, Hassan Nasrallah wanda ya rasa ransa a wani hari da Isara’ilan ta kai a ƙarshen watan Satumba.

A lokacin da aka kai harin, jami’in labaran ya na tsaka da aiki ne a wani ofishin ‘Baath Party’ wanda akwai irinsa a ƙasashen Larabawa da dama inda ya rasa ransa tare da wasu mutane uku, yayin da wasu 14 kuma suka jikkata, kamar yadda hukumomin ƙasar Lebanon suka bayyana.

By Babaji