Aƙalla mutane 25 ne suka mutu, yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti sakamakon ɓarkewar cutar kwalara a ƙananan hukumomin Sokoto North, Silame da Kware a Jihar Sokoto. Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Asabe Balarabe, ta bayyana hakan ga manema labarai a Sokoto, inda ta ce a halin yanzu, jihar tana kula da mutane 15 da aka tabbatar suna ɗauke da cutar a yankunan Sokoto North, Silame da Kware.
A cewar Balarabe, an gano waɗannan mutane 15 da ke ɗauke da cutar ne ta hanyar gwaji. Kuma an tabbatar da cewa suna ɗauke da cutar kwalara.
Ta kuma bayyana cewa mutane 1,160 ne aka ce sun kamu da cutar, inda daga cikinsu, 25 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon kamuwa da wannan cuta. Ta bayyana cewa tawagogin ceto na jihar na aiki tare da gwamnatin jiha domin shawo kan yaɗuwar cutar.
Kwamishinar ta bayyana cewa matakin gwamnatin jihar game da wannan ɓarkewar cuta ya kasance cikin sauri da inganci, inda aka riga aka siyo magunguna da aka rarraba a ƙananan hukumomi 18 a matsayin wani matakin gaggawa don daƙile ci gaba da yaɗuwar cutar.
