Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano
Shugabar gidauniyar USIR, Hajiya Ummasalama Ishaƙa Rabiu, sabuwar Jarumar Hausa da mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk ya naɗa a ranar Asabar da ta gabata, ta bayyana cewa wannan tallafi ba shi ne na farko ba kuma ba shi ne na ƙarshe ba, ta ce duk wanda ya ke ƙasar nan musamman a nan Arewa yana da gudunmawar da mahaifinsu Sheikh Ishaƙa Rabiu Khadimul ƙur’an ya bayar a lokacin rayuwarsa, don haka suka ɗora a inda ya tsaya musamman wajen taimakawa almajirai da sauran mabuƙata, kasancewar su ma almajirai ne masu girmama Alƙur’ani da ahalinsa kamar yadda ta bayyana.
Ta ce za su ci gaba da tallafawa har ƙarshen rayuwarsu da ikon Allah.
Ta bayyana cewa “kowa yasan halin da ake ciki a yanzu da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ke ƙoƙarin ciyar da ƙasar nan gaba, wanda waɗannan tsare-tsare na shugaban ƙasa ya sa mutane na cikin takura amma ba da daɗewa ba al’umma za ta ga alfanun tsare-tsare na shugaban ƙasa don haka a ƙara haƙuri da addu’a jam’iyyarmu ta APC za ta warware matsaloli da yardar Allah.”
Hajiya Ummasalama ta tabbatar da cewa ita ‘yar siyasa ce amma ba ta takarar kowanne muƙami, ta ce burinta dai al’umma ta samu rayuwa mai inganci.
Taron dai ya samu wakilan shugaban ƙasa da kuma wakilan shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa Dr Abdullahi Umar Ganduje da sauransu.
A ƙarshe shi ma shugaban APC na ƙaramar hukumar Gwale Hon. Malam Umar Kashe Kwabo, ya bayyana cewa raba wa mabuƙata kayan sana’o’i da jari da Gidauniyar USIR ta yi na raba wa maza da mata da tallafin kekunan ɗinki, injinan markaɗe da injinan bada hasken wutar lantarki da jari kuɗi da Gidauniyar Ummasalma Ishaƙa Rabiu da ake kira USIR Foundation ta yi abin koyi ne ga mawadata ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da sauran hukumomi da ƙungiyoyi da cibiyoyi a wannan lokaci kamar dai yadda Hon. Malam Umar Kashe Kwabo shugaban jam’iyyar na APC na ƙaramar hukumar Gwale Kano ya bayyana a wurin taron miƙa tallafi ga mutane kimanin 500 da suka samu tallafin jari da kayan sana’o’i wanda aka gabatar a ranar Lahadin nan da ta gabata a Kano.
