Daga MUHAMMADU MUJJITABA A KANO
Shugaban Makarantar Islamiyya da ta zamani na makarantar Sayyadina Usman Bin Affan Liltahfizul ƙur’an Wailari Na’ibawa, ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano, Sheikh Abubakar Ahmad Darma, ya yaba wa mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II, kan karramawa da ya saba yi wa Alƙur’ani da addinin Musulunci hidima na halartar bikin yaye ɗalibai 105 da suka sauke Alƙur’ani mai girma a wannan makaranta mai albarka, inda 15 cikinsu suka haddace Alƙur’ani da iya littattafai guda 5 na Fiƙihu da Hadisi sai kuma guda 90 da suka yi saukar biye domin cigaba da neman karatu da ilimi a rayuwa kamar dai yadda shugaban makarantar ya bayyana a lokacin saukar da ta gabata a harabar makarantar da ke Wailari Kano.
Haka kuma ya bayyana cewa wannan makaranta ta yi sauka karon farko da yara 42 sai kuma wannan sauka karo na 2 wanda ya samu halartar fitattun mutane da sauran al’umma masu nuna kishin ilimi da taimakon addini kamar irinsu Alhaji Kabiru Sani Kwangila Kadimun Nabiyu, irinsu Alhaji Gambo Tanko, Hakimai 13 da shugabannin ƙaramar hukumar Kumbotso da ɗaukacin Dagatai na ƙaramar hukumar da sauransu, sai kuma manyan malamai irinsu Sayyadi Bashir Tijjani Usman Zangon Bare-bari da sauran malamai da al’umma.
A ƙarshe ya bayyana cewa wannan makaranta ta duƙufa wajen tarbiyyar yara matasa da sauran al’umma inda ya yi addu’ar samun kyakyawan shugabancin jiha da ƙasa wanda shi ne ke kawo zaman lafiya, ƙaruwar arziƙi da kwanciyar hankali a Kano, dama duniya baki ɗaya.
