Yi wa mutum tiyata a asibiti ba tare da sa hannun ɗan uwa ba laifi ne babba – DG PHIMA

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Shugaban hukumar kula da asibitoci da cibiyoyin gwaje-gwajen jini da sauran gwaje-gwaje da manyan kantunan sayar da magani da ƙanana da sauran wurare masu alaƙa da harkar lafiya masu zaman kansu, ya bayyana cewa babban laifi ne a yi wa mutum mara lafiya aikin tiyata ba tare da sa hannun wani makusancinsa ba, domin darajar mutum ta wuce a masa irin wannan ba tare da cikakkiyar masaniya ko amincewar ɗan uwansa ba kamar yadda ya ke a ƙa’idar dokar kula da lafiya kamar dai yadda DG PHIMA, Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad ya bayyana a hirarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a tsakiyar makon da ya gabata.

Haka kuma ya bayyana cewa yanzu haka hukumar ta tantance da tabbatar da asibitoci da cibiyoyin gwaje-gwajen biciken lafiya masu zaman kansu a Jihar Kano aƙalla 600, sai kuma kemis-kemis guda 7,000, a yayin da masu magungunan gargajiya suka kai 11000 da hukumar ta horar da masu magungunan gargajiya da kuma shirin basu takardun shaidar horon da aka musu domin saita aikinsu kamar yadda ya dace.

Ya ƙara da cewa daga cikin manyan ayyukan wannan hukuma ta PHIMA akwai kula da asibitoci masu zaman kansu da tantancesu da yi musu rijista da kuma bibiyar aikinsu, sai kuma ɗaukar matakan shari’a ga duk wanda ya karya ƙa’idar kula da dokokin lafiya da aka tsara, wanda yanzu haka akwai asibotoci guda 37 da hukumar ta gano kurakuransu ta rufesu, inda 6 daga cikin 37 suka gyara kuransu aka buɗesu kuma wasu saboda rashin dacewa ko cancanta da su yi aikin lafiya an rufesu har abada, an kuma sanar da dukkanin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki na cewa an haramta waɗannan asibitoci ko cibiyoyin lafiyar da suka buɗe a Jihar Kano.

Haka zalika Farfesa Salisu Ibrahim Ahmad, ya ƙara da cewa kowane asibiti ko wata cibiyar lafiya kafin su amince da ita akwai sharuɗɗa da dama da suke dubawa kafin ba da izini da yi mata rijista, sai sun dubi yanayin tsaftar wuri, yanayin ginin wuri da yawan ma’aikata da ƙwarewarsu sai kayan aiki da dai sauransu, don tabbatar da cewa mai aikin lafiya ya cancanci yin wannan aiki a duk inda za a yi shi.

Haka kuma ya bayana abin mamaki da takaici na yadda wasu masu wannan aiki a asibitoci masu zaman kansu ke nuna haɗama da son zuciya na yin aiki da bai kamata a yi shi a asibitin da suke da shi ba da sauran ƙalubale suke fuskanta na ganin wasu abubuwa da bai dace a gani a wurin da ake kula da lafiya ko binciken lafiya wanda duk wannan shi ke sa hukumar ta ɗauki mataki na doka da sauransu.

A ƙarshe ya yaba wa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, na bada dama hukumar ta samu kayan aiki kamar motocin sufuri kwamfiyutoci da sauransu wanda lokacin da suka zo abin ba daɗin gani ko faɗa, ya yaba wa sauran masu ruwa da tsaki wajen ba wannan hukuma haɗin kai da goyan baya musaman ma’aikatan wannan hukuma irinsu Hajiya Khadija Hussaini Said, Babbar jami’a a hukumar da shugaban ma’aikata Alhaji Alhassan Sani Mai iyali, da Barista Muzakkar Umar Abdullahi, mai kula da harkokin shari’a a hukumar dama ɗaukacin ma’aikata manya da ƙanana da jami’an tsaro na wannan hukuma da sauransu kan nuna kishinsu ga aikin na rashin gajiyawa a kodayaushe.

By ukarofi