Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sake jaddada niyyar gwamnatinsa na magance rikicin da ake fama da shi tsakanin manoma da makiyaya wanda ya yi sanadin rasa rayuka da dama.
Tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya game da samun ruwa da ƙasa a jihohin Nijeriya da dama na barazana ga samar da abinci.
Tinubu ya ce sabon ƙudurinsa na jawo jarin cikin gida da na waje zuwa fannin kiwon dabbobi a cikin harkar noma zai kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya, kawar da yunwa da talauci a Nijeriya tare da inganta ci gaban tattalin arziki.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a Rio de Janeiro, ƙasar Brazil lokacin sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya da JBS S.A, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa naman dabbobi a duniya.
“A halin yanzu abin da muke yi shine magance matsala wadda ta addabi al’umma a wannan yanki na Afirka, rikici tsakanin manoma da makiyaya wanda ya yi sanadin rasa rayuka da zubar da jini, alhali akwai hanyoyin zamani da za a iya warware waɗannan matsalolin har ma a samar da tattalin arziki mai kyau daga gare su,” inji Tinubu a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a.
Tinubu ya yi kira ga kamfanin da ya yi amfani da damar da ke cikin jarin dala biliyan $2.5 da ke cikin fannin kiwon dabbobi a Nijeriya musamman kasancewar tana da yawan jama’a tare da amfani da ƙwarewarsu da aka amince da shi a duniya wajen tabbatar da tsaro na abinci.
Shugaba Tinubu ya shaida wa manyan jami’an JBS cewa Najeriya ta shirya yin kasuwanci da su, tare da ba su tabbacin samun riba mai kyau daga jarinsu.
Kafin ziyararsa zuwa ƙasar Brazil, shugaban ƙasa ya ɗauki tawagar jami’an Nijeriya da masu zaman kansu don amfani da damar taron shugabannin G20 a Rio don gudanar da bincike a Sao Paulo, Brazil, tare da gano damarmaki a fannin bunƙasa kiwon dabbobi, sarrafa nama da cigaba ta fannin iri na shuka.
