
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), ta ce har yanzu ta na kan bakanta na bada wa’adin ranar 1 ga watan Disamba ga gwamnonin da ba su ƙaddamar da sabon mafi ƙarancin albashi ba a jihohinsu.
Kakakin ƙungiyar, Benson Upah ya sanar da hakan a cikin wani saƙon kar-ta-kwana ga manema labarai a Abuja inda ya ce lallai wa’adin ya na nan yadda NLC ta faɗa na 1 ga watan Disamba, 2024.
A yayin haka ne jihohin da ba su kai ga zartar da sabon mafi ƙarancin albashin ga ma’aikacinsu ba ke ƙoƙarin ganin sun yi hakan kafin wa’adin da aka ba su ya cika.
A ranar Litinin ne, mataimakin gwamnan Sakkwato, Alhaji Idris Gobir, a madadin gwamnatin jihar, ya gana da wakilan NLC na jihar inda ya roƙi da su miƙa samfurin gyare-gyaren albashin ga Gwamnatin jihar don dubawa.
Shugaban NLC na jihar, Abdullahi Jungul ya jinjina wa gwamnatin ga ƙoƙarinta na kwaskwarima ga tsarin albashi, ya na mai kira ga ma’aikata da su kwantar da hankulansu inda ya ce za su gaggauta miƙa jaddawalin gyare-gyaren albashin.
Haka ma Gwamantin Zamfara ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara biyan albashi da sabon tsarin albashin, inda a halin yanzu ana cigaba da tantance ma’aikata a jihar.
Idan za a iya tunawa, jihar, ƙarƙashin tsohon gwamna Bello Matawalle, ba ta samu ƙaddamar da biyan mafi ƙarancin albashi na N30,000 ba da aka amince da shi ba a shekarar 2019.
Har’ilayau, Gwamnatin Jihar Taraba ita ma ta yi ikirarin da fara biyan sabon albashin nan ba da jimawa ba, kamar yadda Shugaban ma’aikatan jihar, Paul Maigida ya bayyana.
