
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Sakkwato ta jaddada aniyarta ta inganta harkokin wutar lantarki a jihar ta hanyar kammala aikin tashar lantarki na gashin kanta (IPP).
Gwamna Aliyu Ahmed ya bayyana hakan wa manema labarai jim-kaɗan bayan kammala zaman Majalisar Zartarwa ta jihar a gidan gwamnatin jihar, a ranar Laraba.
Ya ce gwamnatinsu za ta tabbatar da yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kammala aikin tashar wanda ake fatan ya taimaka wajen bunƙasa harkokin tattalin arziƙi a jihar.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa zata bada cikakken goyon baya ga jami’an tsaro a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta’addanci wanda a yanzu haka ana ɗaukar matakan da suka dace wajen ganin an cimma hakan.
Gwamnan, kamar yadda aka wallafa a shafinsa na X, ya ce Majalisar Zartarwar a ƙarƙashin jagorancinsa, ta ƙaddamar da muhimman al’amura jihar waɗanda suka shafi tsaro da ababen more rayuwa da wasu dangogin al’adu a jihar da sauran su, a ƙoƙarinsa na samar da gobe mai kyau ga jihar da al’ummarta.
