
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnatin Jihar Katsina da maraɗin Katsina kuma Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu kurfi da iyalan marigayi Jakada Zakari Ibrahim (Talban Katsina) bisa babban rashin da ya same su.
Shugaban ƙasar, wanda Mataimakinsa, Kashim Shetima ya wakilce shi, ya ziyarci garin Kurfi ne bisa jagorancin gwamnan jihar Dikko Raɗɗa inda ya sauka a gidan Hakimin Kurfi wanda tsohon Ministan Gona, Dakta Sama’ila Mamman Kurfi ya tarbe shi.
Shetima ya bayyana Marigayi Ahmadi Kurfi a matsayin Dattijo kuma fitaccen mutum mai faɗa-a-ji da ake ganin martaba shi a ƙasa Ali ɗaya, ya na mai addu’ar samun rahama a gare shi.
A gidan marigayi Talban Katsina, Sardaunan Katsina kuma tsohon shugaban Hukumar Leƙen Asiri na Ƙasa (NIA) kuma Sardaunan Katsina, Ahmed Rufa’i da Ibrahim Zakari wanda shi ne babban ɗa ga marigayi Talban suka tarbi mataimakin shugaban ƙasar.
A tawagar mataimakin shugaban ƙasa akwai shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje da Ministan Sufuri, Sanata Sa’idu Alƙali da Ministan Gona, Abubakar Kyari da kuma tsohon Ministan Abuja, Aliyu Moddibo.
Da ya ke jawabi, Gwamna Raɗɗa ya yi godiya ga Shugaba Tinubu bisa tawagar da ya turo ƙarƙashin mataimakinsa don ta’aziyar waɗannan mashahuran mutane.
Marigayi maraɗin Katsina ya taba riƙe muƙamin sakataren Hukumar zaɓe ta ƙasa (FEDECO) a alif 1979.
Shi kuma Talban Katsina ya taba riƙe shugaban NIA da kuma ƙaramin ministan Harkokin Waje.
