Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Gwamna Umar Namadi ya yabawa ministar ilimi Dakta Suwaiba Ahmed Ɓaɓura, ya na mai cewa Suwaiba zaɓin Allah ce, shi kawai sila ne na zamanta minista kuma Allah ya sani ya yi hakane ba da wata manufa ba.
Gwamna Namadi ya ƙara da cewa Dr Suwaiba ta na ɗaya daga cikin ma’aikata masu ƙwazo da ake buƙatar su. Tun tana koyarwa a makarantar ilimi da nazarin Arabiyya da Shari’a da ke Ringim a matsayin malama, tana daga cikin malamai masu ƙwazo da hazaƙa.
Ganin ƙwazonta ne yasa muka ga akwai buƙatar mu bayar da sunanta a wannan kujera domin zuwan ta da taimakon da ta ke yi anan gida Jigawa, idan taje can zai ƙaru kuma jama’a za su amfana daga gudunmawar ta.
Jama’a shaidane na irin taimakon da ta keyi daga hawanta wannan kujera zuwa yanzu. Kowa ya sani tana taimakawa al’ummar Jihar Jigawa da maƙota waɗanda ba ‘yan asalin Jihar jigawa ba.
Gwamna Namadi ya faɗi hakane a daidai lokacin da ya amshi tawagar mutanen masarautar Ringim da ƙaramar hukumar Ɓaɓura a fadar gwamnatin jihar a ƙarƙashin jagorancin ita ministar domin nuna farin cikinsu da godiyarsu ga Gwamna Umar Namadi domin ganin an bata kujerar minista.
Da ta ke jawabi a gaban gwamnan, Hajiya Suwaiba Saidu Ahmed tace ta rako iyayenta da yan uwanta ne tare da dubban masoya domin yiwa mai girma gwamna godiya akan muƙamin da aka naɗa ta na ministan ilimi duk da cewar tazo a baya. Amma kasancewar wannan zuwan shima yana da matuƙar muhimmanci shine yasa ta sake zuwa ta Ƙara godiya .
Shima hakimin garin na Ɓaɓura Alh Hadi Mustapha Ɓaɓura ya godewa Gwamna Namadi a kan marawa yarsu baya ta sami kujerar minista, yace wannan abinda Namadi ya yi masu ya nuna yana ƙaunarsu kuma suna tare dashi ɗari bisa ɗari.
Hakimin ya tabbatar da cewar suna tare da Gwamna Namadi kuma a shirye su ke su bashi duk gudunmuwar da yake buƙata ko yaushe. Ya kuma bashi tabbacin za su marawa gwamnatinsa baya wajen ganin ta kai ga nasara a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.
Shima a nasa jawabin shugaban ƙaramar hukumar Ɓaɓura Alh Hamisu Garu ya yabawa Umar Namadi, ya ƙara da cewar al’ummar masarautar Ringim da ƙaramar hukumar Ɓaɓura ba su da bakin da za su yi wa gwamna godiya akan wannan abun arziki da ya yi wa yarsu, sai dai su ce, Allah ya biya shi, ya yi masa sakayya da gidan aljanna Firdausi.
