Matatar mai mallakin Nijeriya da ke Fatakwal ta fara aiki bayan kammala gyaran ta da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tayi tare da sabunta shi. An soma aikin sabunta ta da yi ma ta gyara ne a shekara ta 2021 zamanin mulkin Shugaba Buhari akan kuɗin kwantiragi Dalar Amurka Biliyan 1.5.
Shugaba Tinubu ya cigaba da wannan katafaren aikin tare da tabbatar da cewa ya kammalu, a ƙoƙarin sa na tabbatar da cewa dukkan matatun mai mallakin Nijeriya sun fara aiki ka’in-da-na’in domin ƙara bunƙasa harkar haƙowa da tace man fetur.
