Su waye suke da alhakin durƙusar da Arewa? (II)

Spread the love

To ina so duk mai hankali ya tsaya yayi tunani a kan wannan maganar, dalili kuwa shi ne don ya fahimci su waye matsalar Arewa, kuma su waye suka zamo silar maida Arewa baya? Idan har Bola Ahmad Tinubu shugaban Nijeriya a yanzu zai yi waccan maganar kafin ya zamo shugaban ƙasa, to a yanzu da ya zama gaskiya ya faɗa ko ƙarya? An ce masa ya ya zai yi da matsalolin da suke damun Arewa? Ya ce idan ya ce zai yi wani abu a kai za a kashe shi. To kun ga kenan matsalar da duk ke faruwa a yankin Arewa manyan Arewar ne suka haifar da ita, shi yasa duk tsauraran matakan da shugaban ƙasa Tinubu yake ɗauka basa iya fitowa su ƙalubalance shi kai-tsaye har suyi yunƙurin dakatar dashi, saboda ba su da wannan ikon, domin kuɗi ya basu suka mara masa baya, ba wai don ya cancanta ba, kuma don haka duk abinda yayi babu mai iya hana shi a cikinsu, domin suna da kashi a gindi, ko sun yi magana ba zai saurare su ba.

Wannan shi ne dalilin da yasa talakawa suke mamakin yadda abubuwa ke faruwa amma an kasa dakatar da shugaban Nijeriya Tinubu. Ga babban misalin da talakawan Arewa za su yi la’akari dashi, ana rantsar dashi ya ce, “Subsidy must go” a take ya cire tallafin mai, hakan yasa man ya fara tsada, ba a daɗe ba ya cire tallafi a kan wutar lantarki, ya ƙara haraji, ya cire tallafin abinci, ya karya darajar Naira, dalar Amurka ta riƙa hawa kullum. Wanne babba aka ji ya tsawatar masa a lokacin? A cikin wata ɗaya aka yi ƙarin kuɗin mai har sau uku. Ya sayi sabon jirgin sama, duk manyan Arewar suna nan, kuma suna ganin komai, kuma uwa-uba ma suna tare dashi, amma me ku ka ga sun yi?

Mu ɗauki jihar Kano, iya ƙwaryar birnin Kano tafi jihar Lagos yawa ban da ma ƙananan hukumominta 44, amma Lagos na da cibiyoyin samar da hasken wutar lantarki guda 8, jihar Ogun tana da 6, mu kuma a jihohin Arewa 19 guda biyu kawai muke dasu. Ina manyan Arewar? Ina dattawan Arewar, na majalisa da jami’an tsaron soji da ‘yansanda, tsaffin gwamnoni da waɗanda suke kan kujera? Ina tsaffin ministoci da daraktoci, wanda suke kai da wanda suka yi ritaya? Ina manyan Alƙaƙai da Lauyoyinmu na Arewa? Cin kashin da ake yi mana a Arewa, wulaƙanci da cin mutunci duk basa gani ko kuwa basu sani ba?

A jihar Kano an ɗebi ‘ya’yan musulmi masu yawa an kai su jihohin kudu ana canza musu addini da sunaye, yau saboda rashin haɗin kai irin namu na ‘yan Arewa, manyan Arewa suna gani ana kashe bayin Allah a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Nassarawa da Niger, a kashe, a tare hanya a kwashi mutane a kora daji a nemi kuɗin fansa, a shiga ƙauyuka a kashe, ayi wa mata fyaɗe, a ɗauka a tafi dasu daji sai an biya kuɗi. An san waɗanda suke wannan aiki, ana ganinsu, ana kama su. Amma abin haushi da takaici, wasu sai a kama a saki, wani ma ɗan ta’addan da kans yake bada labarin an kama shi fiye da sau huɗu ko biyar, zai biya kuɗi a sake shi ya ci gaba da abinda yake yi.

To a irin wannan halin da muke ciki a Nijeriya (musamman a yankin Arewa), ina wata rayuwar jin daɗi take a wurin talaka? Saboda yunwa da talaucin da aka ƙaƙaba mana, mutane da yawa sun zama ‘yan ta’adda. Tsanani baya sa mutum ya zamo na kirki a cikin sauƙi, sai dai ma ya ƙara kangarewa. A yayin da talauci yayi yawa a cikin al’umma, to yunwa tana ƙaruwa, duk kuma wanda ke jin yunwa kuma ba shi da abinda zai ci, to zai iya canza tunani daga kyakkyawan tunani zuwa mummuna. Shi yasa Allah Ubangiji (S.W.T) duk da ya haramta cin mushe, amma kuma Allah Yayi umarni ga wanda yake cikin matsananciyar jin yunwa, ya buga bai samu abinci ba, mutane suka ƙi taimakonsa, ga shirya galabaita zai iya rasa rayuwarsa, sai aka ce idan yaga mushe ya ɗauka ya ci (don kada ya mutu).

Allah (S.W.T) Ya faɗa a cikin Alƙur’ani mai girma cewa, “Haƙiƙa ni na haramtawa kaina zalunci, kuma (al’umma) na haramta zalunci a tsakaninku.” Don haka shugabannin al’umma ku sani, wallahi tallahi sai Allah Ya tambaye ku a kan haƙƙin bayinSa da ku ke ci, kuma ku ke ciyar da iyalanku. Wata rana Khalifa Sayyidina Umar (R.A) ya fito yana bin Burtali (hanyar da dabbobi suke wucewa) yana ɗauke ƙaya da duk wani abin cutarwa da hannunsa, sai wani mutum ya ganshi ya tambaye shi “Ya Amirul Muminina, me yasa ka ke wannan aiki da kanka?” Sai Sayyidina Umar (R.A.) ya ce: “Wallahi ina tsoron Jaki ya taka ƙaya, ranar gobe ƙiyama Allah Ya tsaida ni Ya tambaye ni don me na bar Jaki ya taka ƙaya ina matsayin Khalifa”.

A haƙiƙanin gaskiya matsalar da ke damun Arewa da har ta kai girman da ake gani a yanzu, ba kowa ba ne yasa hakan ta faru face shugabanninmu na Arewa. Saboda basa kishin yankin Arewa, basa kishin al’ummar Arewa. Sun fifita buƙatunsu da siyasarsu fiye da rayuwar aminci da salama da al’ummar yankin Arewa ya kamata su samu. ‘Yan siyasa sun siyasantar da al’amurran Arewa, sun zubar da kimar Arewa a idon duniya. Su ne suka lalata matasanmu na Arewa, ta hanyar amfani dasu wajen bangar siyasa, su ne suka lalata jami’an tsaronmu na Arewa, suka maida su karnukan farauta.

Maimakon suyi siyasa ba da gaba ba, sai suka ɗauki siyasa hanyar yaƙar juna a zahiri, tare da lalata al’amura kamar yadda ake gani yanzu.

Jami’in tsaro ba shi da ikon kamawa tare da gurfanar da ɗan siyasa a kan laifi, maimakon haka ma sai ya riƙa sara masa duk da cewa yasan bai cancanta ba. Sarakuna sun zubar da kimarsu ta iyayen ƙasa, Malaman addini sun ɓata kansu wajen suka da faɗa da juna, sun ƙi haɗe kai kamar yadda Allah Ya faɗa, “Ku haɗe kawunanku kada ku rarraba…” ba ga iya malamai kaɗai ayar ke umarni ba, har da mu talakawa mabiya, amma haɗin kai ya kasa samuwa, duk wanda jifa ta wuce kanshi, to kawai ta faɗa kan ɗan uwansa bai damu ba.

Mu a Arewa a halin yanzu babu wani abi da zamu nuna mu bugi ƙirji mu ce muna alfahari dashi na ci gaba da aka samu, tun daga mulkin tsohon shugaban ƙasar Nijeriya Muhammadu Buhari, da wannan mulkin da muke cikinsa a yanzu na shugaba Bola Ahmad Tinubu, domin talakawan Nijeriya sun fita hayyacinsu. Saboda masifa da bala’in ƙuncin rayuwa da aka shiga, matan aure fita suke suna aikata zina ana biyansu don su ci abinci, ‘yan mata ma haka, ballantana zawarawa masu lasisi, kuma duk wannan na da alaƙa da halin da ake ciki. Mace-macen aure ƙaruwa yake, auren kuma ya yi ƙaranci. Kayan masarufi ƙara tashi suke, Nairarmu ƙara lalacewa take, kasuwanni ba ciniki, sace-sace ƙaruwa suke, ta’addanci sai ƙaruwa yake. Maimakon al’umma su tsarkaka su zama nagari, amma kullum mutane sai ƙara shiga aikata miyagun ayyuka suke don kawai su rayu. Wannan kuma duk na faruwa ne saboda shugabanni sun kasa yin adalci ga al’umma, wanda na tabbatar da za su yi adalci, to da komai ya dawo daidai.

Duk wanda ba ya kishin Arewa, to haƙiƙa maƙiyin al’ummar Arewa ne, duk wanda yake ƙaunar Arewa da al’ummar yankin Arewa, to tilas yayi takaicin abubuwan da suke faruwa a yankin Arewa.

‘Yan Arewa muyi karatun ta-nutsu, mu farka tare da miƙe wa tsaye don yin yaƙin dawo da martabar Arewa, ta hanyar ƙauracewa shugabanni marasa adalci, mu samar da shugabanni nagari don rayuwar yaranmu na gobe masu tasowa, don gudun kada su tsinci kansu a halin ƙuncin rayuwar da mu a yanzu muka tsinci kanmu a ciki, saboda rashin kyakkyawan shugabanki.

Daga NAFI’U SALISU. Marubuci/Manazarci, daga Kano Nijeriya. [email protected]@gmail.com. 09056507471-08038981211.

By ukarofi