Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da shirin tallafawa masu buƙata ta musamman

Spread the love


Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), ta hannun Shirin Abinci na Duniya (WFP), ta sanar da wani sabon shirin samar da kaya da nufin bai wa kamfanonin da masu buƙata ta musamman ke jagoranta.

Wannan shirin na daga cikin dabarun tabbatar da daidaito a tsarin samar da kaya ko bada kwangila na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Shugaban Cibiyar Sayen Kaya na Majalisar Ɗinkin Duniya kuma babban jami’i a WFP, Daniel Kuhe, ya bayyana wannan sabon shiri yayin taron tattaunawa kan damammaki ga masu buƙata ta musamman da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba.

Taron ya yi daidai da bikin ranar masu buƙata ta musamman ta duniya da ake gudanarwa a duk ranar 3 ga Disamba.

Kuhe ya bayyana cewa sabon shirin ya ƙunshi gayyatar masu sha’awar shiga kamfanonin da masu buƙata ta musamman ke jagoranta. Ya ce wannan tsari zai taimaka wajen rushe shingayen da ke hana shiga tsarin siyen kaya na MDD tare da ba da dama ta adalci ga duk masu ruwa da tsaki. Ya ƙara da cewa, “Kamfanonin da masu buƙata ta musamman ke jagoranta za su iya neman dama kamar kowane kamfani.”

A yayin taron, shugaban ƙungiyar Accessibility Professionals, Yusuf Iyodo, ya yi ƙarin bayani kan yadda ake ware masu buƙata ta musamman a fannin kasuwanci tun bayan samun ‘yancin kai a Najeriya. Ya buƙaci a samar da tsarin da zai fifita shirin samar da kaya daga kamfanonin da masu buƙata ta musamman ke gudanarwa, musamman a matakin Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma na ƙasa.

Kuhe ya kuma bayyana cewa WFP na shirin ƙaddamar da shirin ba da shawarwari da jagoranci ga kamfanonin da masu buƙata ta musamman ke jagoranta domin su fahimci yadda tsarin samar da kaya na Majalisar Ɗinkin Duniya ke gudana. Ya ce wannan shiri yana da burin tabbatar da daidaito a nan gaba, inda ya ƙara da cewa, “Za mu ci gaba da buɗe ƙofa ga kamfanoni da masu buƙata ta musamman ke jagoranta tare da samar da kayan aiki don taimaka musu wajen samun nasara.”

By ukarofi