Isra’ila na cigaba da kisan Falasɗinawa – Amnesty International

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar Amnesty International ta bayyana yaƙin da Isra’ila da Amurka ke yi wa al’ummar Falasɗinawa a matsayin kisan ƙare dangi. A cewar kungiyar, “wannan mummunan al’amari ya kamata ya zama abin farkawa ga al’ummar duniya: wannan shi ne kisan kare dangi. Dole a dakatar da shi yanzu.” Tun daga fara wannan yaƙin a Gaza kwanaki 426 da suka wuce, rahotanni sun nuna cewa mutane 44,466 ne suka rasa rayukansu, tare da 105,358 da suka samu raunuka, yawancinsu mata da yara. Duk da haka, har yanzu dubban mutane suna maƙale ƙarƙashin baraguzan gine-gine.

Rahoton ya kuma bayyana cewa mutane 11,900 ne aka kama a yankunan Falasɗinawa, ciki har da yara 790 da mata 435, yayin da 10,000 daga cikinsu ke tsare ba tare da gurfanarwa ba. Hakanan, tasirin yaƙin ya ƙara dagula rayuwar al’umma, inda farashin kayan abinci a Gaza ya karu da sama da kashi 1000% idan aka kwatanta da farashin da aka saba a baya. Rahoton Ofishin Kula da Al’amuran Jin Ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya (OCHA) ya ce daga watan Oktoba 2023 zuwa Oktoba 2024, mutane 736 sun mutu a Yammacin gaɓar kogin Jordan, ciki har da yara 170.

Bugu da ƙari, yara sun fi shan wahala a wannan rikici, inda aka kwantar da yara 19,000 a asibitoci cikin watanni huɗu kawai saboda ƙarancin abinci mai gina jiki. Gaza yanzu ta zama yankin da ke da mafi yawan yara masu nakasu na jiki a duniya. Hakan na faruwa ne yayin da ake gudanar da tiyata ba tare da amfani da maganin kawar da zafi ba. A ƙarƙashin rikicin, mutane 130,000, mafi yawansu mata da yara, sun tsere daga Arewacin Gaza zuwa Kudu, inda suke fama da rashin wurin kwana, barazana ga cin zarafi da matsalolin lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa tallafin jin ƙai ya samu cikas sosai a Gaza. Tsakanin 1 zuwa 25 ga Nuwamba, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi yunƙurin kai tallafi sau 41 zuwa yankunan da aka killace a Arewacin Gaza, amma sau 37 daga ciki an hana su kai tallafin kwata-kwata. Ko da aka amince da wasu, shingen soji ya hana tallafin isa ga mutanen da ke cikin wahala. Duk da haka, an amince da motocin tallafi 1,489 kawai su shiga Gaza, wanda ke nufin motocin tallafi 65 a kullum, kwatankwacin kashi 13 cikin 100 na abin da aka yarda kafin rikicin ya fara.

Haka kuma, Isra’ila ta bayyana aniyarta na ƙwace abubuwan kiran sallah daga masallatai, tana cewa kiran sallah yana damun mazauna Yahudawa kuma yana haifar da “barazana” ga al’umma. Wannan mataki ya zo ne tare da buƙatar cewa a ci tara ga waɗanda suka yi amfani da lasifika a masallatai. Wannan lamari yana ƙara nuna tsananin danniya da nuna wariya kan Falasɗinawa, musamman a yankunan da ake ci gaba da mamaye su.

By ukarofi