Shiyyar Kano ta samu sabon Mataimakin Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shiyya ta ɗaya da ta haɗa Kano da Jigawa ta samu sabon mataimakin shugaban rudunar ‘yan sandan Nijeriya, AIG Ahmed Ammani Malumfashi, wanda ya bayyana ƙudirinsa na cewa zai haɗa kai da shugabannin al’umma a kowane mataki da su kansu al’ummar tun daga ƙasa a matakin unguwanni da ƙauyuka na yankunan karkara da birane domin tabbatar da ingantaccen tsaro a wannan shiya ta Kano kamar yadda shugaban ‘yan sandan Nijeriya IGP Kayode Egbetokun, ya naɗa shi a wannan aiki na mataimakin ‘yan sandan Nijeriya, mai kula da Kano da Jigawa.

AIG Malumfashi ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke tare da manyan jami’ai ‘yan sanda da ke wannan shiyya a a ofishinsa dake shelkwatar ‘yan sanda shiyya ta ɗaya da ke Kano, inda kuma ya yaba wa ‘yan sandan Nijeriya kan wannan dama da ya bashi na yi wa al’ummar ƙasa hidima.

Bugu da ƙari ya ƙara da cewa kan cimma wannan burin a tabbatar da tsaro a wannan shiyya rundunar ‘yan sandan za ta ƙara yawan zirga-zirga a tsakanin al’umma da kuma dabaru da hikimomi na aiki domin zaƙulo masu aikata laifuffuka, kamar ‘yan daba da sauran masu karya doka.

Haka kuma ya tabbatar da cewa za a kare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda doka ta ɗora musu a kowane lokaci za mu yi aiki dare da rana domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kowane lokaci.

Bayanai sun tabbatar da cewa an haifi mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya Ahmed Malumfashi, 11 Mayu, 1965 a Jihar Katsina Unguwar Galadanci da ke ƙaramar Hukumar Malumfashi da ke jihar, ya fara karatu tun daga Firamare har zuwa Digirin Digirgir da sauran kwasa-kwasai inda ya yi firamare ta Warure Kano daga shekarar 1971 zuwa 1977, sai Sakandiran Wudil 1977 zuwa 1982, sai ya yi babbar kwalejin karatu mai zurfi ta Zariya 1982 zuwa 1984, HKU 2004.

Jami’ar Bayero ya fara 1984 zuwa 198, sai ABU Zariya 2008 zuwa 2010, da sauransu, ya kuma riƙe makamai a rudunar ‘yan sanda da dama a jihohin Nijeriya irin, Nassarawa, Zamfara, Abuja, Ondo, kuma shi ne mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya na 25 a wannan shiyya ta ɗaya da ta haɗa Kano da Jigawa, tun ranar 29 Nuwamba na 2024.

By ukarofi