Gwamnatin Kano ta yaba wa Ifing Media da One17 bisa taro kan harkar kuɗi a Musulunci

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Cibiyar Ifing Media ƙarƙashin shugabancin Mudathir Adesanya, da kuma Alhaji Zakari Ahmadu, shugaban cibiyar hadadar kuɗi ta Musulunci na One17 da ke najeriya sakamakon shirya taron da aka yi wa take da wayar da kan al’ummar Arewa akan hadadar kuɗi a Musulunci irinsa na farko da aka yi a Arewacin Nijeriya da aka kira Arewa Islamic Finance Summit, wanda cibiyoyin hadadar kuɗi na Musulunci suka halarta tare da manyan masana na cikin gida da na wajen Nijeriya, da aka gabatar da maƙaloli kan tasiri  da muhimmancin hadadar kuɗi a Musulunci wajen kawo cigaban ƙasa da zaman lafiya a ƙasa wanda ya gudana a Kano a ranar Litinin da ta gabata.

A jawabinsa gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin Sheikh Tijjani Sani Auwalu, kwamishinan al’amuran addini na Jihar Kano da gwamnatin Kano, ta yaba da wannan ƙoƙari wajen wayar da kan al’umma kan yadda ake hadadar kuɗi, musamman yadda Jihar Kano ta yi shura a kan yawan Musulmi da yawan ‘yan kasuwa, ilimi, noma, sarauta, da sauransu wanda Kano na buƙatar wannan tsari domin cigaban Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Shi ma Alhaji Zakari Ahmadu shugaban One17, ya ce wannan taro alkairi ne babba ga al’umma kuma za a samu cigaba mai yawa a wannan tsari musamman su da karɓar wannan shiri zai sa, su ƙara faɗaɗa hadadar su a lungu da saƙo na Nijeriya ga kuma damar da za a samu wajen cigaban kasuwanci mai tsafta da ƙara yawan ma’aikata inda ya yaba wa shugaban haɗa wannan taro Alhaji Mudathir da sauran masu ruwa da tsaki.     

A ƙarshe Alhaji Musa Yau shugaban ƙungiyar masu sai da katako na ƙasa reshen masarautar Haɗeja, na daga cikin ‘yan kasuwa daga Jihar Jigawa, da aka gayyata wannan taron wayar da kai na Arewa akan harkar kuɗi a Musulunci, ya ce wannan taro irinsa na farko sun amfana da ilimi mai yawa, kamar yadda Alhaji Aminu AA Aljazira babban manomi kuma ɗan kasuwa shi ma ya bayyana haka a wajen wannan taro da a ka gabatar na kwana biyu a Kano.

By ukarofi