Za mu gudanar da ayyukan cigaban al’ummar Rimin Gado – Salisu Rimin Gado

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Shugaban ƙaramar Hukumar Rimin Gado a Jihar Kano, Hon. Sani Salisu ya bayyana ɗan majalisar jiha mai wakilatar Rimin Gado da Tofa a Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Muhammad Bello ɓutuɓutu da cewa shugaba ne abin koyi da duk wanda yake shugabanci zai so ya yi koyi da halayensa nagari.

Ya ce duk wanda ya san shi ba abinda zai faɗa maka sai halayensa na kirki ba kaɗai a Rimin Gado da Tofa ba hatta a jihar Kano baki ɗaya duk, wanda ya san shi, zai gaya maka mutumin kirki ne mai magana ɗaya idan kaje gidansa a ranekun ƙarshen mako za ka samu sama da mutum 100 maza da mata ba sai in ana wata hidima ba, talakawa ne daga yankunan ƙananan hukumomin da yake wakilta suke kawo kokensu da matsalolinsu.

Ya ce a tarihin Rimin Gado da Tofa ba a taɓa samun ɗan majalisar jiha da je majalisa a jere sau uku ba sai akan Hon. Muhammad Bello ɓutuɓutu aka fara saboda aminta da al’umma da su kayi da irin ayyuka da ake na alkhairi  da mu’amala da talakawansa da yake.

Hon. Sani Salisu ya yi nuni da cewa shi ma da ya koyi siyasa daga ɗan majalisar a matsayinsa na jagoransu, ga shi Allah ya sa ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado za su cigaba da koyi da shi a siyasa kuma suna da tsare-tsaren gudanar da muhimman ayyuka na cigaban al’ummar ƙaramar hukumar Rimi Gado.

Shugaban ƙaramar hukumar na Rimin Gado Hon. Sani Salisu Rimin Gado ya ce al’ummar ƙaramar hukumar Rimin Gado a cikin wata ɗaya da ya soma jan ragamar shugabanci sun tsara da kawo abubuwa na cigaba da haɗin kai da mutunta juna da soma samar wa yara makarantu na ɓangaren kula da lafiya, sannan sun shirya yin ayyuka da yawa da za su kawowa ƙaramar hukumar ci gaba da yardar Allah.

By ukarofi